Ana ci gaba da fuskantar karancin kwan gidan gona a Jihar Neja, biyo bayan rufe gidajen gona da ake ci gaba da yi a fadin jihar.
Wannan dai ya afku ne, sakamakon tsadar kayan abincin kajin da masu sana’ar ke ci gaba da fuskanta.
Rahotanni sun bayyana cewa, kwan kajin gidan gonar da ake turo wa zuwa jihar, musamman daga Jihar Oyo ya yi matukar raguwa, saboda tsadar da man fetur ya yi bayan cire tallafin man da Gwamnatin Tarayya ta yi.
Haka zalika, an ruwaito cewa yanzu farashin kowane kiret guda da ake sayo wa daga gidan gona a jihar, ya doshi naira 2,200 sabanin yadda ake sayar da shi a baya kan naira 1,800.
Har ila yau, akwai kuma kalubalen rashin kyakkyawan yanayi da ke shafar yawan kwan da ya kamata a samu a gidan gona, wanda haka ke sa kajin na mutuwa.
Wani mai sayen kwan, mai suna Isah Suleiman ya bayyana cewa, ya zagaya zuwa shaguna da dama don sayen kwan, amma bai samu ba.
Shi kuwa wani mai saye da sayar da kwan da ke Kasuwar Tunga a jihar, mai suna Christopher Ukaegbu ya bayyana cewa, kwan ya yi karanci a duk fadin jihar; kusan sama da mako biyu da suka wuce.
Shi ma wani manajan kajin gidan gonar da ke garin Minna a jihar ta Neja, Mista Adeyemo Adewale ya bayyana cewa, an samu karancin kwan da kuma tsadarsa a makon da ya gabata tare da tashin farashin abincinsu.
Bugu da kari, Mista Adeyemo ya ce, gidan gona da dama a jihar ta Neja da ake kiwon kajin gidan gonan; yawancinsu sun rufe, musamman saboda tsadar abincin da ake ciyar da kajin da kuma kwan da wasu manyan gidan gona da ke kawo wa Jihar Neja daga Jihar Oyo, sun dakatar sakamakon tsadar man fetur ya yi.
Adeyemo ya ci gaba da cewa, a kwanan baya wani gidan gona da yake a garin Minna, da ake kiwata kajin gidan gona wanda yawansu ya kai 3,000, tuni an rufe shi sakamakon wannan tsada ta abincin kaji, hatta mu ma da muka ci gaba da yin kiwon muna kokarin ne kawai, in ji shi.
A cewarsa, buhu daya na abincin kajin da muke saya a kan naira 8,500 a watan da ya wuce, yanzu kowane buhu ya tashi zuwa Naira 9,500.
Haka nan, masu gidan gonar da suka ci gaba da kiwata kajin, sun gaza samar da yawan qwan da ake bukata a kasuwanni, inda sauran mutane kuma ke ci gaba da nuna bukatarsu ta kwan.
Ya kara da cewa, a yanzu haka a gidan gonar tasa ba za a iya samar da bukatar qwan da mutane ke bukata ba na kaso 50 cikin 100 ba, inda ya ce, wasu masu zuwa gonar don sayen kwan, na far zuwa ne tun misalin karfe biyar na Asuba, domin sayen kwan da kuma kaji wadanda aka kyankyashe.
“Gidajen gona da dama da ake kiwon kaji a jihar, sun rufe sannan kuma kwan da ake kawo wa jihar daga kudancin kasar nan, ya ragu sakamakon tsadar da man fetur ya yi, sannan akasari, mun dogara ne a kan man dizel da muke zuba wa injin janareto,” in ji shi.
Saboda haka, a yanzu farashin man dizel ya karu daga naira 750 zuwa Naira 1, 050 kowace lita, wanda hakan ya kara jawo rufe gidajen gonar da ake kiwata wadannan kaji.
Shi ma wani manajan gidan gona da ake kiwata kaji na gidan gonar lSani Ahmadu, ya danganta karancin kwan kan wannan tsada ta man fetur da kuma tashin farashin abincinsu.
Kazalika ya kara da cewa, bukatar da ake da ita ta kwan a fadin jihar, ta fi karfin gidan gonar su iya samar da yawan kwan da ake bukata a jihar.
“Bukatar na da yawan gaske kuma ba mu da qwan da ake bukata a halin yanzu, ya kara da cewa, zuwan masu yi wa kasa hidima a sansaninsu da ke jihar, ya kara bukatar kwan a sansanin.
Source LEADERSHIPHAUSA