Mataimakin shugaban kasa, Kasheem Shettima, a ranar Talata, yayin da yake tsokaci kan tabarbarewar darajar Naira, ya bayyana cewa “mafi mawuyacin halin da aka shiga ya kare” ga matsalar kudin Nijeriya.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da gasar zane da kirkire-kirkire ta kasa a Abuja, Kasheem Shettima, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Stanley Nkwocha ya fitar, ya bayyana kwarin gwiwar cewa, Naira za ta ci gaba da farfadowa a cikin makonni da watanni masu zuwa.
Da yake jawabi a kan matsalolin tattalin arziki, mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, “mafi mawuyacin halin da aka shiga ya kare”, inda ya kara da cewa, Naira za ta ci gaba da farfadowa a cikin makonni da watanni masu zuwa, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke magance matsalolin da suka shafi karancin abinci da rashin tsaro.
A wani labarin na daban shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da bai wa sojoji 17 da aka yi wa kisan gilla a yankin Neja Delta lambar girmamawa ta kasa da kuma alkawarin gina wa kowanne gida a inda suke so tare da bai wa ‘yayansu tallafin karatu har zuwa matakin jami’a.
Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin gudanar da jana’izar sojojin sojoji 17, inda ya bayar da umarnin cewar hukumomin soji su tabbatar da cewar an biya hakkokin wadannan soji nan da wata uku.
Tinubu ya bayyana cewar shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya masa bayani a kan irin gagarumar gudumawar da Laftanar Kanar Ali, kwamandan sojin da aka kashe ya bayar wajen yaki da Boko Haram da kuma ‘yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma, kafin mayar da shi yankin Neja Delta.
Shugaban ya ce a madadin Nijeriya yana mika sakon jinjina ga Kanar Ali saboda yadda ya bayar da gagarumar gudumawa a rundunar sojin har zuwa lokacin da aka masa kisan gillar.
Tinubu ya ce a matsayinsa na babban kwamandan sojin Nijeriya baki daya, yana sane da irin gudumawar da bajintar da sojojin suka bayar wajen tabbatar da tsaron Nijeriya.
Shugaban ya ce duniya na sane da rawar da sojojin Nijeriya ke takawa a Afirka da kuma wasu sassan duniya, saboda haka ba za su bar iyalansu su taggayara ba.
DUBA NAN: Dalibai Sun Rasa Rayukan Su A Cinkoson Karbar Taimakon Abinci A Jami’ar Nasarawa
Jana’izar ta samu halartar manyan hafsoshin tsaro da ministoci da iyalan sojojin da aka kashe