A jawabin da ya gabatar ta kafafen yada labarai a ranar Litinin ga al’ummar Nijeriya, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce, gwammatinsa ta dauki wasu muhimman matakan da za su kawo karshen matsatsi da al’ummar kasa ke ciki sakamakon janye tallatin Mai.
A cewarsa, za bai wa masu masana’antu 75 jari mai rangwame har na naira biliyan daya kowannen su, wanda za su biya a tsahon watanni 60 cikin hanyoyi mafi sauki.
Kazalika, shugaban ya ce, masu matsakaita da kananan sana’o’i za su amfana da naira biliyan 125 domin habbaka jarinsu.
Kazalika, daga cikin waccan biliyan 125 gwamnati za ta bada jari kyauta (mai hade da sharadi) na naira 50,000 ga masu kananan sana’o’i mutum 1,300 a kowace karamar hukuma.
Sannan, sauran biliyan 75 za su tafi wajen masu matsakaitan sana’o’i inda za a bai wa mutum 100,000 rance mai rangwame na naira 500,000 zuwa miliyan ɗaya wanda za su biya a hankali cikin shakara uku.
Shugaban kasan ya bada umarnin fito da abinci har Ton 200,000 tare da takin zamani Ton 225,000 domin rabawa ga mabukata da manoma a fadin kasar nan.
Dukka a jawabin nasa, ya ce, nan ba da jimawa ba gwamnati za ta samar da kananan moticin bus masu amfani da gas har guda 3,000 domin kawo rangwame a kudin sufuri da jama’a ke fama da shi. Wadannan motoci za a raba su ne ga kamfanonin sufuri domin gudanar da su.
Haka nan kuma gwamnati ta ware makudan kudade domin noma hekta 500,000 a banagarori daban-daban na ƙasar nan. Baya ga samar da abinci wannan shiri zai samarwa da matasa marasa aikin yi sana’a ta wucin-gadi.
Tare da gaggauta aiwatar da tsarin gyaran albashin ma’aikata da zarar gwamnati ta cimma matsayi da kungiyoyin kwadago.