Bankin Duniya ya yi a hasashen bunkasar tattalin arzikin Nijeriya a shekarar 2024 daga hasashen da ya yi na kashi 2.9 a watan Oktoba na shekarar da ta gabata zuwa kashi 3.3 a wannan shekara da kuma kashi 3.7 a shekarar 2025, kamar dai yadda rahotonsa na watan Janairun 2024 ya nuna.
Ana hasashen tattalin arzikin duniya zai yi kasa a karshen shekarar 2024, wannan kuma shi ne tafiyar hawainiyar Mfi girma da aka samu a cikin shekara 30, kamar dai yadda mujallar bankin duniya mai suna ‘Global Economic Prospects’ ta nuna.
Bankin Duniyan ya yi wannan hasashen ne tare dda fatan tsare-tsaren tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke gudanarwa a kasa za su haifar da da mai ido. Duk da cewa, tana da tunanin za a samu koma bayan tattalin arziki a duniya, shekara uku a jere, kashi 2.4 kafin kuma ya koma kashi 2.7 a shekarar 2025.
Rahoton ya nuna cewa, za a samu bunkasar tattalin a rziki a wannan shekarar na kashi 3.3 zai kuma karu zuwa kashi 3.7 a shekarar 2025, wannan na faruwa ne saboda ganin matakan bunkasar tattalin arzikin na da gwamnati ke yin a kara bayyana.
“An yi hasashen ne da fatan tattalin arzikin kasa zai bunkasa tare da gudummawa da tallafin harkar aikin gona, gine-gine, da kuma kasuwanci. Za kuma a samu saukin hauhawar farashi saboda matsin da janye tallafin man fetur ya haifar zai ragu a hankali.
Haka kuma abubuwan da za su taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin Nijeriya a wannan shekarar sun hada da fitar da wasu kayyakin da ake sarrafawa a gida zuwa kasashen waje da kuma sake fasallin farashin kayayyaki a hankali ta yadda al’uimma za su shiga saye da sayarwa don bunkasa tattalin arzikin su.
“An kuma samu bunkasa yanayin rayuwar al’umma, musamman yadda aka samu kwanciyar hankali a tafiyar da tsarin dimokradiyya a Nijeriya da ma nahiyar Afirka gaba daya”, in ji rahoton.
Source: LEADERSHIPHAUSA