Kamar yadda ko wani hanyoyin ke da amfani da rashin anfanin sa, haka yanar gizo shima yana da dimbin amfani da kuma rashin anfani (wato advantages da kuma disadvantages).
A wannan makon zan kawo mana wasu daga cikin anfanin yanar gizo, daga karshe kuma zan kar kare da wasu daga cikin Illoli ko kuma rashin anfanin da yawan Ta’ammuli da shi ke jawo wa.
A lokutan baya karni na 16 zuwa kasa, babu kayoyin sadarwa na zamani kalan wadanda muke amfani da su a yanzu. Lokacin akwai Wayar salula wanda ake anfani da ita a ofis ko a gida, ba kalan wanda muke anfani da ita yanzu ba wanda zaka iya fito ko ina da ita a cikin aljihun ka.
A wancan lokacin kamar yadda na ambata a ofis ne kawai ake anfani dashi, ko kuma wanda suke da halin siyowa su ajiye a cikin gidajensu.
Duba da irin yanayin wancan lokacin da hanyoyin ba kowa ke iya anfani da Wayar salulan ba, dalili kuwa shi ne, wasu basu da kudin da za su siya, saboda akwai tsada sosai, ko kuma saboda karancin ilimin yadda ake sarrafa shi.
Mafiyawan masu Ta’ammuli da kayan sadarwa a wancan lokacin wayayyu ne, kuma masu ilimi. Mafi akasarin su ‘yan jami’a ne.
Saboda haka, suna da zuzzurfan fahimtar yadda hanyoyin suke da kuma yadda yakamata suyi amfani da shi. Suna iya fahimtar illolin shi da kuma lokutan da ya kamata, da kuma lokutan da bai kamata su yi amfani dashi ba. Haka kuma a Makarantun su ana Wayar da su akan yadda za su cigaba da amfani wadannan abubuwa.
Abin takaicin shi ne a wannan lokacin da kayan sadarwa na zamani suka yawaita, lokacin da aka fi bukatar wayar da kan al’umma su fahimci yadda ake sarrafa irin wadannan kayyakin, kuma su fahimci illoli da kuma alfanun shi, a lokacin ne kuma Wayar da kan ya yi karanci sosai. Shiyasa mutane ke fadawa ciki ba tare da sanin hakikanin yadda yakamata su yi anfani dashi ba.
Kamar yadda na fada a baya a lokutan da suka gabata a ofis ne kawai ake anfani da kwamputoci da Wayar salula, sai kuma gidajen masu hannu da shuni. Zaka samu a ofis ofis din da ake da kwamputa, akwai kwarrarun da suke kulawa da wannan sashin.
Amma daga karni na goma sha tara (19th century) lokacin kwanfutoci suka yawaita, kuma masu amfani dasu suma suka yawaita. A kowane gida sai ka samu masu amfani da kwanfuta ko kuma wayar hannu. Saboda haka wasu na anfani da su ta hanyar da ta dace, wasu kuma na anfani da su ta hanyar da bai dace ba.
Akwai hanyoyi da dama dake kara dadin masu amfani da wayar hannu da kwanfuta, kuma su ne manhajojin sadarwa na zamani irin su facebook, Whatsapp, Twitter, Instagram, da sauransu. Kuma saboda su ne mutane ke bata lokacin su suna danna waya domin duba sakonni da kuma aikawa da nasu sakonnin.
Ba aika sakonni ne kawai dalilin kirkiro hanyoyin manhajojin sadarwa na zamani ba, akwai hanyoyi da dama da idan muka bi, za mu ci moriyar kafofin sadarwan. Misali; kwanakin baya Facebook ta kirkiro da wani bangare da cikin bangarorin manhajan, wanda suka yi wa lakabi da ; “Market Place”.
A Marketplace din sun bada daman tallata kayyakin daban daban domin samun masu siya. Wannan ba karamin taimakawa zai yi ba wajen bunkasa harkokin kasuwanci na yau da kullum. Ba Facebook kawai bane suka kebanta da wannan sashi ba, Sauran manhajoji Kaman Twitter, Instagram, Tik Tok, YouTube, da sauransu.
Babban abun takaicin shi ne; duk da yadda wadannan manhajoji da kuma websites suke bada dama domin anfani da su ta hanyoyi daban daban wadanda suka da ce, amma wasu ba’adi na mutane na anfani da su ta hanyoyin da basu kamata ba. Misali; “Facebook” mafi aksarin mutane sun dauka facebook kawai dandali ne na tura sakonni da kuma kallon hotunan da daura nasu hotonunan domin samun ”like” da “comments”.
Zaka ji har tambaya akeyi “like” nawa ka samu ?. Ba ina cewa kar ayi “chatting” bane, abun da nake kokarin nuna wa shi ne kar mu bari ‘chatting’ din ya hana mu yin wasu abubuwan da suka fi shi muhimmanci, a ciki da wajen facebook din.
Musamman matasa masu wuni da kwana a facebook, whatsapp, Twitter, Instagram, da makamatansu.
Yakamata su san cewa suna da abin da yafi su zauna suna chatting din muhimmanci.
Zaka ga dalibi dan jami’a yana karatu, amma idan ya rike waye baya iya ajiyewa, wasu na wuce karfe daya na dare suna “online” kuma da gari ya waye za su tashi su daura daga inda suka tsaya.
Idan ka ce zaka biye ma anfani da wadannan hanyoyin manhajojin na sadarwa, to babu shakka ka dauko ruwan dafa kanka, domin kuwa ka auri siyan “Data” kenan kullum kana neman yadda zaka yi ka samu kudin “data”. Hakazalika dole zaka kulla abota da chaji idan idan chajin kudi ne, zaka yi ta cacan kudin chaji kamar yadda kake siyan “Data”.
Buga da ari kuma akwai hanyoyin “websites” da dama da ko yaushe a shirye suke domin taimakawa dalibai ko kuma masu bincike da bayanan da suke bukata, amma matasanmu basu maida hankali akan su wani idan ka tambayeshi bai san anfanin ‘google’ ba sai kallon hotuna da bideo.
Akwai wasu websites din kuma da suke koyar da Karatu kyauta kuma idan ka kammala zasu baka satifikate din kammalawa.
Daga karshe, a Wannan dan takaitaccen rubutun ba zan samu daman kawo mana duk abubuwan nayi niyyan kawo wa ba, kiran da nake Dashi ga matasanmu shine yakamata su fahimci yadda zasu ci moriyar yanar gizo, bai Kamata ya zama kullum kana siyan Data amma tana tafiya a iska ba.