Gwamna El-Rufai ya sallami ma’aikata 60,000 daga aiki a kasa da shekara shida na mulkin sa.
Femi Falana da ASCAB sun ce an kori Ma’aikata kusan 60, 000 a Jihar Kaduna – Idan hakan ya tabbata, gwamna Nasir El-Rufai yana korar ma’aikata 280 kullum.
Femi Falana yace korar Ma’aikatan da ake yi ne ya jawo matsalar rashin tsaro Fitaccen lauya mai kare hakkin Bil Adama, Femi Falana da kungiyar Alliance on Surviving COVID-19 and Beyond sun soki gwamnatin jihar Kaduna.
Femi Falana da kungiyar ASCAB sun bayyana cewa gwamna Nasir El-Rufai ya sallami ma’aikata 60, 000 tun bayan da ya karbi mulkin Kaduna a Mayun 2015.
Alliance on Surviving COVID-19 and Beyond da Femi Falana SAN sun nuna goyon bayansu a kan yajin-aikin da kungiyoyin kwadago su ka soma a Kaduna.
A wani jawabi da kungiyar ASCAB ta fitar a ranar Lahadi, ta yi kira ga duk wadanda suke karkashin kungiyar kwadago ta NLC su shiga wannan yajin-aikin.
ASCAB ta ce sai an yi da gaske domin ayi maganin sallamar tulin ma’aikata da talauci da halin rashin tsaron da aka jefa al’ummar jihar Kaduna a gwamnatin APC.
Femi Falana ya ce tun fil azal, ma’aikatan gwamnati da na masaku ne suka rike tattalin arzikin Kaduna.
Jaridar Punch ce ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin. Falana yake cewa a shekarun bayan nan ne duk wadannan matatu suka mutu, aka kori ma’aikata daga aiki da-dama ba tare da an biya su wasu hakkokin sallama ba.
Lauyan ya ce a maimakon gwamna Nasir El-Rufai ya yi maganin wannan matsala, sai ya kori ma’aikata kusan 60, 000, sannan aka hana mafi yawansu hakkin su.
“Jihar Kaduna ta na da hadarin zama ko aiki a Najeriya, a dalilin yawan kashe-kashe, garkuwa da mutane, zubar da jini, rikicin kabilanci da addini.” Inji Falana SAN.
Har ila yau, Lauyan ya ce ana fama da matsalar tsaro ne saboda yawan korar mutane daga aiki da gwamnati ta ke yi, ya ce keta hakkin ma’aikata ne ya haddasa hakan. Lauyan ya ce an kori ma’aikata 13, 000 a 2016, sannan aka sallami wasu 40, 000 a 2017.
Daga nan gwamna el rufa’i ya fatattaki malamai 21, 000, a bana kuma an kori ma’aikata 17, 000. Kawo yanzu akwai ma’aikata 11, 000 da gwamnati ta shirya za ta kora daga aiki, a cewar Falana.