Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), ta tirela guda 21 makare da kayan abinci da za a fitar zuwa kasashen ketare.
EFCC ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata da daddare a shafinta na Intanet.
Ta ce jami’anta sun kama tirelolin ne a kan hanyar Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama da ke Jihar Borno.
“Ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2024, jami’an EFCC shiyyar Maiduguri sun kama manyan motoci guda 21 makare da kayan abinci da kuma wadanda ba na abinci ba a kan hanyarsu ta zuwa birnin N’djamena na kasar Chadi, da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Kamaru,” in ji sanarwar.
Kamar yadda jaridar Leadership ta rawaito EFCC ta kara da cewa bincikenta ya gano cewa “an yi dabara ne aka boye kayan abincin a cikin manyan motocin ta yadda ba za a gane ba, amma ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen gano ba.”
Ta ce an soma gudanar da bincike kan mutanen da aka kama a cikin manyan motocin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala binciken.
“Ana sa rai kamen da aka yi wa motocin zai rage karancin abincin da ake fama da shi a fadin kasar nan sakamakon ayyukan fasa-kwauri.”
Gwamnatin Tarayya ta zargi masu fasa-kwauri na da hannu a tashin farashin kayan abinci a Nijeriya.
A watan da ya gabata, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce an kama manyan motoci guda 45 dauke da kayan abinci da za a fitar daga kasar nan.
DUBA NAN: Najeriya Zata Daina Hada Hadar Binance
Ya kara da cewa sun gano barauniyar hanya guda 32 da ake fitar da abinci daga Nijeriya.
Har yanzu dai ana ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci a Nijeriya.