A kasuwar gwamnati darajar naira ta dan samu cigaba idan aka kwatanta da baya inda ta kai N1,551.24 duk dala daya idan aka kwatanta da N1,574.24 da take a da kamar yadda Nigerian Autonomous Exchange Market suka sanar da Sahara Reporters.
Tattalin arzikin Najeriya dai na cigaba da samun ruqushi.
A ranar talata an sayar da dala a kan 1,900 a Abuja a Kano da legas kuma 1,800 pound din Ingila kuma ana samun sa a N2,250.
Sahara Reporters ta rawaito cewa, hukumomin da alhakin yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ke hannun suna suna ta kai samame matattarar ‘yan canji dake Abuja, Kano Lagos da kuma fatakwal.
Mai bawa shugaban kasa shawara Nuhu Ribadu a rahoton Daily Trust ranar talata ya umarci rundunar ‘yan sanda, kwastam da sauran wadanda abin ya shafa su fara samame a matattarar masu canjin kudi domin daukan matakan kalubalantar rashin dai dai a bangaren.
See Also: Atiku Ya Fadi Mafita Dangane Da Halin Da Ake Ciki
Jaridar Reuters ta rawaito cewa, gwamnan babban bankin Najeriya Olayemi Cardoso ya tabbatarwa da majalisar kasa cewa, an samu karin fiye da dala biliyan da a tattalin arzikin Najeriya inda inda aka sayi Treasury Bills bayan a sayar da fiye da triliyan guda na naira.
Gwaman babban bankin ya tabbatarwa da ‘yan majalisa cewa, matakan da da babban bankin ya dauka domin farfafo da darajar nairar ya kalubalanci rushewar darajar kudin.