Rahotanni daga jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa daliban makarantar Kwalejin gwamnati ta Yauri 30 da malami ɗaya sun kubuta daga hannun ‘yan bindigar da suka sace su a watan Yunin bara.
Sanarwar da mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kebbi kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ya aike wa manema labarai, ta ce tuni aka mika su ga hukumomin lafiya domin duba lafiyarsu, kuma daga bisani za a sada su da iyayensu.
Shi ma mai bai wa gwamnan jihar shawara kan sha’anin tsaro Garba Rabi’u, ya shaida wa BBC cewa an kubutar da daliban ba tare da an biya kudin fansa ba, yana mai cewa suna cikin koshin lafiya.
Sai dai ya ce har yanzu akwai sauran daliban da ke hannun ‘yan bindigar, wadanda su ma ake sa ran kubutar da su nan ba da jimawa ba, a cewar hukumomi.
A ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba 2021 wasu daliban makarantar Yauri suka kubuta, inda aka mika su ga gwamnatin jihar daga bisani aka sada su da iyayensu.
A ranar 16 ga watan Yunin shekarar 2021 ne ‘yan bindigar suka sace wadannan dalibai sama da 100 daga makarantarsu da kuma wasu malamai suka nausa daji da su.
Satar mutane domin neman kuin fansa, musamman dalibai matsala ce da ta addabi hukumomin Najeriyar ta kuma zama ruwan dare a fadin kasar.
A shekarun da suka gabata satar daliban makaranta da ta ja ha nkalin duniya, ita ce ta dalibai mata na sakandaren Chibo da ke jihar Bornoi da mayakan Boko Haram suka sace.
A bangare guda kuma hukumomin Najeriyar su na ikirarin daukar mataki da nasara a yakin da suke yi da masu tayar da kayar baya na Boko Haram, da ISWAP da kuma barayin daji da masu satar mutane domin neman kudin fansa.