Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da karin kwanaki goma kan wa’adin da ya bayar tun farko na daina amfani da tsoffin takardun naira.
Gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Lahadi, ya ce, ya samu sahalewa da amincewar Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan kara wa’adin.
Yanzu ranar daina amfani da tsoffin takardun kudadem ta koma ranar 10 ga watan Fabrairu sabanin 31 ga watan Janairu da CBN ta sanar tunda farko.
Emefiele, ya yi wannan maganar ne a Daura ta jihar Katsina bayan ya gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Lahadi.
Gwamnan bankin ya yinkira ga ‘yan Nijeriya da ba su sami zarafin canza takardar kudadensu daga tsoho zuwa sabo ba to ga dama ta samu ta yin hakan.
Gwamnan CBN ya jawo hankalin Jama’a da su tabbatar sun yi amfani da wannan damar da aka ba su na karin wa’adin, yana mai cewa bayan wannan kwanaki 10 da suka kara tabbas ba za su sake karawa ba kuma.
LEADERSHIP HAUSA ta labarto cewa babban bankin Nijeriya cikin watan Oktoba ya gabata ya kaddamar da sabbin takardun kudade na 200, 500 da 1000 tare da ware ranar 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar daina amfani da tsoffin takardar kudaden.
A wani bangare kuma zakuji abubuwan 5 Da Zaku So Ku Ji A Ganawar Gwamnan CBN Da Shugaba Buhari A Daura
* Sauya Kuɗi: masu tarin maƙudan kuɗi kadai na halas kamar ‘Yan Kasuwa kaɗai aka ƙarawa wa’adi daga 10 zuwa 17 ga fabarairu.
* CBN ya ce sun samu nasarar sauya tsoffin kuɗi da kashi 75 cikin 100 zuwa yau Lahadi 29, ga Janairun 2023.
* A 2015, Tsabar kuɗi tiriliyan 1.4 kaɗai ke yawo hannun jama’a, abin ya ninninka zuwa 3.23 a shekarar 2022 – Rahoton CBN.
Source:LegitHausa