Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yaki sanya hannu akan sabuwar dokar zaben da majalisa ta amince da ita wadda zata baiwa jama’a damar tsayawa zabe ba tare da neman ubangida ba da kuma aikewa da sakamakon zabe kai tsaye daga tashoshin da aka gudanar da zaben.
Wannan ya biyo bayan cikar wa’adin sanya hannu akan daftarin da Majalisa ta mika masa na kwanaki 30 jiya lahadi, abinda ke nuna cewar shugaban ba zai rattaba hannu akan sabuwar dokar ba.
Ya zuwa wannan lokaci fadar shugaban kasar bata ce komai ba dangane da sanya hannu akan dokar, duk da rahotanni da aka bayar a kwanakin baya cewar shugaban kasar ya nemi shawarar Hukumar zabe wadda ta bashi shawarar sanya hannu akai.
Ita dai wannan sabuwar dokar wadda shugabannin Majalisa da ‘Yan Najeriya da dama suka yi ta bayyana farin cikin su akan ta, ana saran ta bude kofar tsayawa takara ba tare da neman ubangida ba, yadda kowa zai gwada farin jinin sa a gaban jama’a tare da shirin aikewa da sakamakon zabe kai tsaye daga tashoshin da aka kada kuri’u.
A karkashin sabuwar dokar, masu zabe zasu suyi layi ne a bainar jama’a a bayan ‘dan takarar da suke so a karkashin tsarin da ake kira kato-bayan-kato.
Wasu daga cikin ‘Yan Najeriya na kira ga Majalisar dokoki da tayi amfani da karfin da kundin tsarin mulki ya bata wajen amincewa da dokar ta hanyar kada kuri’a kashi biyu bisa uku.
Rahotanni na zargin gwamnonin jihohin kasar da adawa da wannan sabuwar dokar saboda yadda zata rage musu karfin fada aji wajen tsayar da ‘yan takarar kowacce kujera da ake takarar ta, abinda ke basu damar wadanda suke so a matakai daban daban na siyasar Najeriya.
Bayan amincewa da dokar, gwamnonin sun bayyana adawar su da ita, inda suka bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kaucewa sanya hannu akai, saboda wasu dalilai da suka gabatar na kashin kan su.
Wannan ne dalilin da ya sa shugabannin Majalisar dokoki da suka hada da na Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawal da takwaran sa na wakilai Femi Gbajabiamila suka ziyarci shugaban kasar a lokuta daban daban domin janyo hankalin sa akan muhimmancin dokar ga ‘yan Najeriya da kuma dimokiradiya baki daya.
Bayan ganawa da shugaba Buhari, Gbajabiamila ya bayyana cewar shugaban na goyan bayan dokar inda ya bayyana yakinin sa cewar zai rattaba hannu akai.
Tuni wasu daga cikin ‘Yan majalisun suka fara tauna tsakuwa inda suke bayyana aniyar amincewa da dokar ba tare da sanya hannun shugaban kasa, wanda suke zargi da amfani da shirin kada kuri’ar kato-bayan-kato da kuma bijire masa yanzu.