Hukumar kula da asusun taimakekeniyar kiwon lafiya ta jihar Bauchi (BASHCMA), ta kimtsa domin shigar da mutum miliyan biyu cikin tsari domin su samu cin gajiya, hakan, wani mataki ne na kyautata kiwon lafiya a tsakanin jama’a musamman masu fama da matsatsin tattalin arziki.
Wakilinmu ya labarto cewa, shirin na da manufar taimaka wa kiwon lafiyan mutane da ke da ƙaramin ƙarfi musamman ‘yan kasuwa, manoma, da sauran masu gudanar da ƙananan sana’o’i.
Babban sakataren hukumar, Dakta Mansur Dada, shi ne ya shaida hakan lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin mutum 34 da aka ɗaura wa alhakin shigar da mutanen cikin shirin a ofishinsa.
Kwamitin ya haɗa da ma’aikatan BASHCMA, jami’an kula da shirin a ƙananan hukumomi 20, haɗi da sauran jami’an da lamarin ya shafa da ake sa ran za su faɗaɗa shiri ta yadda jama’a za su samu sauƙin shiga a dama da su domin cin gajiyar shirin.
Dada, ya kuma yi fatan cewa za a samu asalin talakawan da sdaa dace su shiga shirin ta hanyar wayar da kai da faɗakar da su muhimmancin shiga tsarin domin kyautata kiwon lafiya.
Dada ya ƙara da cewa, kwamitin na da damar tuntuɓar masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomi domin tabbatar da inganci gami da tabbatar da inganta kiwon lafiya yadda ya dace.
Source: LEADERSHIPHAUSA