Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Dr. Barau I. Jibrin, ya ƙaddamar da motocin bas guda 107 na kamfanin sufuri na Kano ta Arewa.
Wannan shiri dai na daga cikin ƙoƙarin ɗan majalisar na inganta harkokin sufuri a yankin mazabar Kano ta Arewa da ma faɗin jihar Kano.
Za a rarraba motocin bas ɗin ne ga waɗanda za su ci gajiyar tallafin a kan kuɗi kaɗan a ƙarƙashin tsarin haya don mallaka. Waɗanda suka fara cin gajiyar shirin sun haɗa da ƴan ƙungiyar ma’aikatan sufurin mota ta ƙasa (NURTW) daga dukkan ƙananan hukumomin jihar Kano ta Arewa.
Ana sa rai wannan tsarin zai inganta fannin sufuri na cikin gida da kuma haɓaka tattalin arziki ga ma’aikatan sufurin da iyalansu.
Taron ƙaddamar da motocin bas 107 ɗin ya gudana ne a sabon filin wasa na Bichi da ke garin Bichi, wanda ɗimbin jama’a suka nuna jin daɗinsu kan wannan tsari.
A wani labarin na daban gwamnatin Jihar Filato ta yi zargin cewa ta bankado wani shiri da ake yi na rantsar da ‘yan majalisa 16 da suka yi takara a karkashin Jam’iyyar APC a zaben 2023 ta barauniyar hanya a Majalisar Dokokin Jihar.
Gwamnatin jihar dai ta lashi takobin tabbatar da bin tsarin mulki bayan hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ya bai wa bangaren APC nasara.
Tun a safiyar yau Talata, LEADERSHIP ta ruwaito yadda ‘yansanda suka hana wata taho-mu-gama a tsakanin magoya bayan ‘yan takarar APC da kuma ‘yan majalisar PDP da kotu ta kora, a yayin da suka yi yunkurin shiga zauren majalisar da karfin tuwo.
Mai bai wa Gwamna Caleb Mutfwang na jihar ta Filato shawara a kan yada labarai, Timothy Golu ya bayyana yunkurin a matsayin abin bakin ciki wanda ya zo wa gwamnatin jihar da mamaki.
“Mun wayi gari kawai muka ga jami’an tsaro a kewayen zauren majalisar jiha. Ka san majalisar ba ta gudanar da zamanta a gininta na asali, an sauya mata wuri zuwa fadar gwamnatin jiha saboda gyaran da ake yi a can…
“Idan da akwai wani abu da ya taso, da shugaban majalisar ya kira zaman majalisar amma kuma duk da haka shi a halin yanzu tamkar an sa masa mari ne saboda akwai umarnin kotu biyu da aka ba shi da suka hana rantsar da ‘yan majalisa 16 da Kotun Koli ta ba su nasara, sannan a matsayin gwamnati ta mai bin doka ba za mu bari wani ya zo da wargi ba har sai an soke wadancan umarnin.”
DUBA NAN: Hukumar Alhazai Ta Bayyana Lokacin Da Za’a Kammala Aikin Hajin Bana
Saboda haka a cewar Timothy, hallarar jami’an tsaro a ginin majalisar wata barazana ce da ba za su amince da ita ba, domin wata munakisa ce ta rantsar da ‘yan takarar APC 16 ta barauniyar hanya.