Bankin Duniya ya ce ana sa ran bunkasar tattalin arzikin yankin kudu da hamadar sahara zai ragu a bana, sakamakon faduwar darajar kudi da ake samu a kasashen Afirka ta Kudu da Nijeriya da kuma Angola.
Bankin ya ce, ci gaban tattalin arzikin yankin zai ragu zuwa kaso 2.5 a cikin 2023 daga 3.6% da aka samu a bara.
Bisa ga dukkan alamu, yankin bai samu wani ci gaba mai kyau ba tun daga shekarar 2015, saboda ayyukan tattalin arzikin kasashen yankin ya kasa tafiya daidai da karuwar al’umma da ake samu.
Babban masanin tattalin arziki a bankin Afirka, Andrew Dabalen, ya shaida wa AFP cewa, masu fama da talauci da marasa galihu a yankin na ci gaba da fuskantar matsalar tattalin arziki sakamakon koma baya, sakamakon ci karuwar rashin ayyukan yi da ake samu.
Tattalin arzikin nahiyar da ya fi samun ci gaba, Afirka ta Kudu, wadda ke fuskantar matsalar makamashi mafi muni a tarihi, ana sa ran zai bunkasa da kashi 0.5% a bana.
Ana sa ran bunkasar tattalin arziki a manyan kasashen da ke hako mai wato irin su Nijeriya da Angola zai ragu zuwa kashi 2.9% ko kuma kashi 1.3.
A wani labarin na daban fadar shugaban Nijeriya a karon farko, ta yi watsi da zargin da ake yi cewa takardar shaidar kammala karatu da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bogi ce.
Idan dai ba a manta ba, a cikin wannan makon ne Jami’ar Chicago da ke kasar Amurka ta fitar da takardun karatun Tinubu, bayan umarnin wata kotun kasar a hukuncin da ta yanke kan karar da dan takarar jam’iyar PDP a zaben da ya gabata na 2023, Atiku Abubakar, ya shigar don samun karin hujja game da zargin sahihancin takardun karatunsa.
Duk da cewar takardar shekarar karatun Tinubu da jami’ar ta Chicago ta fitar, ba ta dauke da ranar haihuwarsa da kuma jinsi da dai sauransu, hakan ya sa ke bude wani sabon babin takaddamar da ake yi kan takardun karatun shugaba Tinubu.
Sai dai a martanin da mai taimaka wa Tinubu wajen hulda da kafafen yada labarai, Temitope Ajayi ya fitar a shafinsa na X (Twitter), ya ce jami’ar ta tabbatar da karatun da Tinubu ya yi a cikinta.
Hadimin shugaban, ya ce tabbatar da karutu a jami’ar da ta yi, ya nuna babu gaskiya ko kadan a zargin da ake yi cewar takardun karatun Tinubu na bogi ne.
Source LEADERSHIPHAUSA