Babbar jam’iyyar adawa ta Gambia UDP, ta shigar da kara kotu tana kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 4 ga watan Disamba.
Yayin ganawa da manema labarai, lauyan babbar jam’iyyar adawar Borry S. Touray, ya ce sun bukaci kotu da ta soke sakamakon zaben da shugaba Adama Barrow ya lashe.
‘Yan adawar na Gambia sun shigar da karar tasu ce ba tare da sanarwa ba, lamarin da ya sa bayan samun labara daga bisani ‘yan jarida suka shafe awanni a harabar kotun da ke Banjul sun dakon fitowar wakilan jam’iyyar UDP, inda daya daga cikinsu ya shaidawa RFI cewa suna kokarin kaucewa jawo jama’a zuwa kotu.
A wani labarin na daban shugaban Gambia mai ci Adama Barrow na kan gaba a samakon farko na wasu yankuna da aka fitar bayan zaben ranar Asabar dake matsayin zakaran gwajin dafi ga demokradiyar kasar bayan Yaya Jameh.
Wani jami’in hukumar zaben ya shaidawa manema labarai a Banjul babban birnin kasar cewa ya kamata a bayyana sakamakon karshe da yammacin wannan Lahadi.