Marigayi Janar Sani Abacha ya yi mulkin Najeriya daga 1993 zuwa 1998 da ya mutu, yana daga cikin adadin shugabannin Najeriya da suka mutu kan ragamar mulki.
Tun bayar mutuwar sa, Najeriya na cigaba da gano wasu adadin kudade da ya boye a kasashen waje wanda aka fi sani da kudin satar Abacha.
Wannan rahoto na lissafa adadin kudaden satar Abacha da aka samu nasarar kwatowa daga wadannan kasashe:
1. Abdulsalami Abubakar ($750 million) Abdulsalami Abubakar ya dane karagar mulki bayan mutuwar Abacha a 1998 kuma ya shirya komawar Najeriya mulkin Demokradiyya. Ya kwato kudi $750 million daga wajen iyalan Abacha.
2. Olusegun Obasanjo Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya tsakanin 1999 da 2007. A shekarar 2000, ya kwato kudi $64 million da Abacha ya boye a kasar Swizalan. Obasanjo ya kwato $1.2 billion ta wani harka na iyalan Abacha a 2002.
A 2003, Obasanjo ya sake kwato kudade $160 million daga Jersey da Birtaniya, sannan $88 million daga Swizalan. A 2005, Obasanjo ya sake kwato $461 million daga Swizalan, hakazalika a 2006 $44 million. Daga lokacin AbdulSalam zua Yanzu: Adadin kudin satar Abacha da aka samu nasarar kwatowa Source: Getty Images
3. Goodluck Jonathan A 2014, tsohon shugaban Jonathan ya smau nasarar kwato $227 million daga kasar Liechtenstein
4. Muhammadu Buhari A 2018, Shugaba Muhammadu Buhari ya kwato $322 million daga Swizalan, sannan a 2020, ya samu nasarar kwato $308 million daga Jersey/USA. Jimillar kudaden badakalar Abacha da aka kwato kawo yanzu = $3.624 billion.
Amma abin tambayar shine duk wadannan tarin adadin kudade da ake ikirarin an karbo suna ina?
Domin dai talakawa suna shan bakar wahala ne a wannan yanayin da ake ciki amma an kasa debo wadancan makudan kudade domin a samar da yanayi mai kyau wanda talaka zai yawa kuma ya tabbatar ya sha romon dimokoradiya.
Najeriya na ckin kasashen da mutanen ta ke cikin bakin talauci tare da yalwar ma’adanai da arzikin da Allah ya hore wa kasar ta bangarori da dama, ana sa ran a samu canji a rayuwar ‘yan najeriya indai da gaske wadannan mila milan kudi da aka ambata a kwai su kuma a shirye ake ayi ma al’umma aiki dasu.