Rahotanni daga jihar Kano na nuni da cewa aƙalla mutum 64 ne suka jikkata lokacin da wata tankar mai ta fashe a Sharaɗa.
An gano cewa da yawa daga cikin waɗanda abun ya shafa sun zo kallon yadda motar ta faɗi ne kafin daga baya ta fashe.
Hukumar kashe wuta a jihar Kano, ta tabbatar da faruwar lamarin, tace jami’anta takwas na cikin waɗanda abun ya shafa Aƙalla mutum 64 ne sukaji raunuka kala daban-daban bayan wata motar dakon mai ta fashe a jihar Kano.
Dailytrsut ta ruwaito cewa tankar man fetur ɗin ta fashe sannan ta kama da wuta yayin da take sauke mai a gidan man Al-Hisan dake titin Ali Gusau, unguwar Sharaɗa cikin garin Kano.
Daga cikin waɗanda suka samu raunin akwai jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano waɗanda suka kawo ɗauki cikin gaggawa, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike Rahoto ya bayyana cewa mafi yawan waɗanda suka samu raunukan mazaunan unguwar ne.
An gano cewa waɗanda suka samu raunin sun zo kallon yadda motar ta faɗi kuma take ci da wuta kafin daga bisa ni ta fashe.
Duk da cewa babu wanda ya rasa rayuwarsa, amma aƙalla mutum 64 ne suka jikkata kuma yanzun haka suna amsar kulawa a asibitin Murtala dake Kano.
Kakakin hukumar kashe wuta ta jihar, Saminu Yusuf Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace aƙalla jami’an hukumar 8 na cikin mutum 64 da abun ya shafa.
A wani labarin kuma Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya tsige sarkin Pauwan Katsina hakimin ƙanƙara daga muƙaminsa.
Sarkin ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan gano cewa hakimin na da hannu a hare-haren da yan bindiga ke kaiwa jihar.
Indai hakane aƙalla malaman kungiyar wahabiyanci da yawa suna bukatara a dakatar dasu daga ayyukan wa’azi domin goyon bayan wahabiyanci da suke yi.