Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kuma shugaban tawagar masu tattaunawa dangane da daukewa kasar Iran takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dora mata, Ali Bakiri ya bayyana cewa daukewa kasarsa takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dora mata shi ne mabudin nasara a tattaunawar da ke gudana a halin yanzu a birnin Vienna na kasar Autria.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Bakiri yana fadara haka a halin yanzu dai abubuwa biyu ne tattaunwa zagaye na 8 ta sa a gaba, da farko dagewa Iran wadannan takunkuman da kuma yerje mata da tabbatar da cewa an dagesu din. Idan wadanan sun samu, to kome yana iya bin baya.
Bakiri ya kara da cewa a halin yanzu dai bangarorin da suke halattan taron na kasashen Turai da kuma rasha da China duk sun amince da wannan bukatar kuma ana aiki a kansa.