Gwamnan Jihar Barno dake Najeriya Babagana Umara Zulum ya bankado yadda wasu jami’an kula da lafiya a asibitin gwamnati ke karbar kudaden da suka kai naira dubu 10 daga hannun marasa lafiyar da ya kamata a duba su kyauta.
Sanarwar tace gwamnan ya gayyaci kwamishiniyar lafiya Juliana Bitrus wadda ta raka shi asibitocin da suka ziyarta cikin dare inda suka gano ana aikata wannan aika aikan.
Gusau yace daga cikin asibitocin da Zulum ya ziyarta akwai asibitin Gwange II dake Maiduguri inda ya ga ma’aikatan sa na karbar tsakanin naira dubu 8 zuwa dubu 10 kafin duba marasa lafiyar da kuma basu maganin cutar zazzabin cizon sauro.
Gwamnan ya bada umurni ga hukumar kula da lafiya ta Jihar da ta gudanar da bincike mai zurfi akan lamarin domin gano wadanda suke da hannu a ciki domin hukunta su.
Zulum yace abin takaici ne yadda wasu asibitocin ke da jami’in kula da lafiya guda kawai yana aiki, yayin da a rubuce ake da sunayen ma’aikata 29 dake karbar albashi.
Sanarwar tace gwamna zulum ya kuma bayyana farin cikin sa da yadda ya ga jami’an kula da lafiya na gudanar da ayyukan su cikin natsuwa a asibitin Gwange I ba tare da karbar kudi ba, inda ya jinjina musu.
Wannan dai ba wani sabon abu bane yadda Gwamna Zulum ke kai ziyarar bazata makarantu da asibitoci da kuma ofisoshin gwamnati domin ganewa idan sa halin da ake ciki