Fitattatun jaruman Kannywood suna goyon bayan Tinubu a matsayin ‘dan takarar shugaban kasar da zasu marawa baya a zaben watan Fabrairu.
Sun yi alkawarin goya masa baya, saboda yadda Tinubu ya kawo cigaba sosai ga jihar Legas ba tare da dubi da addinin kowa bako kabila.
Daga karshe, sun bukaci dumbin masoyansu na yankin Arewa-maso-yamma da su fito su kadawa ‘dan takarar kuri’unsu.
Manyan taurarin Kannywood, wadanda suka hada da Ali Nuhu, Adam Zango, Sadiq Sani, Rabi’u Daushe, da saura da dama, sun fito fili sun marawa ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar APC, Bola Tinubu baya.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, taurarin Kannywood din sun bayyana yadda suke goyon bayan Tinubu a zaben shugaban kasa na watan Fabrairu.
Zango, wanda da farko yake goyon bayan ‘dan takarar jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, daga bisani ya sauya sheke zuwa sansanin Tinubu yayin zagayen APC a gidan wasan Sani Abacha a Kano.
Tinubu ya nemi goyon bayan mazauna jihohin Arewa maso yamma, inda jaruman Kannywood suka fi yawan mabiya daga jihohin arewa da suke da dumbin hausawa.
Tsohon gwamnan jihar Legas, a ranar Talata da Laraba, ya tattara dumbin magoya baya daga jihohi bakwai na yankin Arewa-maso-yamma a tarin ayyukan kamfen dinsa.
Tinubu yayi alkawarin dawo da masana’antun da suka mutu a kasar tare da taimakawa wajen magance matsalar gararambar yara a matsayin almajirai idan aka zabesa a matsayin shugaban kasa a zaben watan Fabrairu.
Yayin da dubbannin masoya da magoya baya suke jira tare kosawa su ga ‘dan takarar shugaban kasar a gidan wasannin na Sani Abacha, jaruman Kannywood sun nishadantar da magoya bayan da wakoki da wasannin kwaikwayo yayin da suke neman a goyi bayan Tinubu. Ali Nuhu, wanda ake kira da Sarkin Kannywood, yayi jawabi a madadin abokan aikinsa a wajen taron.
“Ba muyi mamakin ganin irin tarin mutanen da suka hallarci kamfen din ba, saboda hakan na da nasaba da cigaban da gwamna Abdullahi Ganduje ya kawo.
Haka zalika, irin wannan cigaban ne Tinubu ya samar a Legas yayin da yayi gwamnan Legas.
“Tinubu ne ya taimaka wajen cigaban Legas ba tare da duba da addinin kowa ba.
Wannan shi ne dalilin da yasa muke kira gareku da ku fito ku saka masa kuri’u da Nasir Gawuna da dukkan ‘yan takarar APC na Kano.” – Cewar Ali Nuhu.
Sauran jaruman da suka halarci wurin gami da marawa Tinubu baya sun hada da darakta kuma jarumi Falalu Dorayi; jarumi kuma S.A din Ganduje Mustapha Naburaska; jarumin barkwanci Suleiman Bosho; Jarumin barkwanci Baba Ari; jarumin barkwaci Dangwari; da sauransu.
Buhari ya gana da Aisha Binani
A wani labari na daban, shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Aisha Binani ta jihar Adamawa, jarumar mata ‘yar takarar gwamna ta jihar.
A taron da suka yi, Sanata Abdullahi Adamu tare da ministan harkokin mata, Paulin Tallen sun halarta.