Zan tsaya takarar shugaban ƙasa_Tambuwal
A jiya Litinin ne Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya baiyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023 a ƙarƙashin babbar jam’iyar adawa ta PDP.
Tambuwal ya bayyana aniyar ta sa ne a wani taron masu ruwa da tsaki na PDP da ya gudana a birnin Sokoto. Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin tsayawa takarar ne duba da tarihin siyasarsa da kuma yadda ake ta kiraye kirayen ya fito neman shugabancin Najeriya.
Tambuwal ya ce lokacin da Ƴan Majalisar Wakilai ta 7 su ka tuntuɓe shi ya tsaya takarar Kakakin Majalisar, sai da ya basu wasu sharuɗɗa.
Ya ƙara da cewa da ga cikin sharuɗɗan da ya basu shine cewa a matsayin sa na ɗa mai biyayya ga manya a Sokoto, su je su tuntuɓe su da neman shawararsu.
Tambuwal ya ce da su ka je su ka yi tuntuɓa da neman shawarar manyan, sai su ka amince kuma da ga ƙarshe ya samu nasara zama Kakakin.
“to yanzu ma hakane. Na ji kiraye-kirayen manyan jam’iya, mata da matasa da sauran yan jam’iyar PDP a Sokoto na in fara shirye-shiryen tuntuɓar.
“Za mu yi hakan ne da niyyar tsayawa takara a jam’iyar PDP kuma idan Allah Ya amince, sai mu samu shugabancin ƙasar nan.
“Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai, za mu fara tuntuɓa da neman shawara domin tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2023,” in ji shi.