Ahmadu Haruna Dan Zago yana ganin yaudarar kai ne cewa jam’iyyar APC za ta zarce a Jihar Kano.
Duk da yana cikin ‘yan jam’iyyar APC, ‘dan siyasar ya ce da wahala a fasa rantsar da Abba Kabir Yusuf Ambasada.
Dan Zago ya ce mutuwa ko yi juyin mulki kadai ne za su hana NNPP kafa Gwamnati a 2023.
Dan Zago wanda yana cikin jagororin jam’iyyar APC a jihar Kano, ya fadakar da mutanensa da cewa su zama wayayyu.
A wata zantawa da ya yi da gidan rediyon Nasara FM, ‘dan siyasar ya ce yaudarar kai ne kurum a rika tunanin APC za ta zarce a kan mulki a Kano.
Ambasada Ahmadu Haruna Dan Zago ya nuna babu ta yadda za a fasa rantsar da Abba Kabir Yusuf, a nada Nasiru Yusuf Gawuna a madadinsa.
A matsayinsa na gogagge, Dan Zago ya ce ana neman maida ‘ya ‘yan APC jahilai, wawaye ko dakikai, har ma yana neman zama masu abin kunya.
Jagoran na APC yake cewa dokar kasar nan da tsarin mulki sun ce bayan kwanaki bakwai da ayyana zabe, duk wanda bai gamsu ba ya garzaya kotu.
An rahoto Dan Zago yana cewa in dai ba kotun koli ta ruguza nasarar jam’iyyar NNPP, babu yadda za a warware rantsar da Abba Kabir Yusuf da za ayi.
Me zai hana rantsar da Abba?
Tun da an yi zabe, kuma an bada takardar shaidar nasara, ana jiran rantsuwa, mu na da hankali, mu ba jahilai ba ne.
Abin da za su hana a rantsar da Abba a Kano; Ko dai ya mutu ko kuma an yi juyin mulki a Najeriya.
Idan Allah ya karbi kwanansa, dama ‘Dan Adam ne shi kuma duk mai rai mamaci. Ko kuma juyin mulki aka yi a Najeriya, aka jingine tsarin mulkin.
Amma ina tabbatar maka ba a yin Kantoma a gwamna. Sai dai idan an kafa gwamnatin riko na gaggawa, ita ma watanni shida ta ke ciki.
Amma idan an yi zabe babu wata karya da za ayi wa mutane cewa ba za a rantsar da shi ba.