Yau aka cika shekara guda da juyin mulkin da ya kawo karshen dimokiradiya a kasar Myanmar, lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi.
A jawabin shugaban sojin Min Aung Hlaing da aka wallafa yau yace tilasta musu akayi suka karbi iko sakamakon magudin zaben da aka tafka wanda ya bai wa jam’iyyar Suu Kyi nasara.
Shugaban ya yi alkawarin gudanar da karbabben zabe a watan Agustan shekara mai zuwa muddin aka samu zaman lafiya a kasar.
Tuni aka yanke wa Suu Kyi hukuncin daurin shekara 6 a gidan yari saboda samun ta da laifin shigar da na’urar magana ta barauniyar hanya da tinzira jama’a yi wa sojojin bore da kuma karya dokokin yaki da annobar korona.
An sa ran Suu Kyi ta sake fuskantar shari’a a kan zargin shirya magudin zabe lokacin da jam’iyyar ta samu gagarumar nasara a zaben shekarar 2020.
A wani labarin na daban Sabuwar Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya a Myanmar ta bayyana damuwarta kan yadda tashe-tashen hankula ke kara ta’azzaara a kasar, yayin da ta bukaci tsagaita musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan adawar kasar.
Kawo yanzu, an gaza samun cikakkiyar matsaya wajen maganance rikicin kasar duk da yunkurin diflomasiyar da aka yi karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Kasashen Kudancin Asiya.
Manyan Janar-janar na sojin Mynamar sun ki amincewa su yi zaman sulhu da bangaren ‘yan adawar kasar.
A jawabinta na farko tun bayan darewa kan sabon mukaminta, jakadiyar Majalisar Dinkin Duniyar a Myanmar, Noeleen Heyzer ta ce, ta kadu da abin da ke ci gaba da wakana a kasar musamman a jihar Kayin.
Ta kuma yi kira ga daukacin bangarorin kasar da su amince a isar da kayayyakin jin-kai ga mabukata da suka ha da wadanda suka tsere daga muhallansu.
A bangare guda, Kungiyar Save the Children ta tabbatar cewa, an kashe biyu daga cikin jami’anta a jajibirin ranar bikin Kirismati a wani kisan kare dangi da ake zargin sojojin Myanmar da aikatawa a kasar.