Masu neman takarar kujerar shugaban majalisar dattawa na ci gaba da kamun kafa a wajen takwarorinsu.
Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari ya ki janyewa Godswill Akpabio kamar yadda wasu daga cikin manyan yan takarar kujerar suka yi.
Zuwa yanzu, Davida Umahi da Ali Ndume sun hakura da takarar kujerar sun koma bayan Akpabio bisa umurnin Bola Tinubu.
Gabannin rantsar da majalisar tarayya ta gaba, tikitin hadin gwiwa na tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio da Sanata Bauaru Jibrin sun samu sa hannu 61, Daily Trust ta rahoto.
Hakan na zuwa ne yayin da aka ce tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, wanda shima yana neman takarar kujarer, ya nace sai ya yi takarar kujerar majalisar dattawa ta 10, wanda ake sa ran rantsarwa a ranar 13 ga watan Yuni.
Wani babban sanata wanda ya kasance daya daga cikin masu jagorantar sansanin Akpabio/Barau, ya bayyanawa jaridar cewa zababbun sanatocin 61 sun fito ne daga fadin jam’iyyu daban-daban.
Sahara Reporters ta rahoto cewar Akpabio da Barau na daga cikin yan takara tara da ke neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10.
Yari ya yi biris da umurnin Tinubu Majiyoyin sun kuma bayyana cewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci daya daga cikin manyan yan takarar, Sanata Ali Ndume, da ya hakura da takararsa sannan ya marawa tikitin Akpabio/Barau baya wanda ya yarda da hakan.
Ya ce: “Zababben shugaban kasar ya sammaci Ndume sannan ya bukace shi da ya janyewa Akpabio don ra’ayin kasa, adalci da daidaito a bangaren addini wanda ya aikata hakan.
“Ya kuma dage cewa Ndume ne ya kamata ya zama kan gaba wajen tabbatar da Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa na gaba. Ta haka ne muka fara tattara sa hannun.
“Har yanzu muna tantuba, tattaunawa da karbar sa hannu.
Zuwa yanzu, mun karbi sa hannu 61 a fadin jam’iyyu.” Dan majalisar ya ce duk wani kokari na ganin tsohon gwamnan na Zamfara ya janye ya ci tura.
Sai dai kuma, wata majiya ta ce suna harin samun sa hannu 70 kafin rantsar da majalisar.
Ya ce domin shawo kan sanatocin don su dare kujarar, zababben shugaban kasar ya ce ya kamata tikitin Akpabio/Barau ya zo ta hanyar hadin gwiwa.
Shugabancin majalisar dattawa: Gwamna David Umahi ya janyewa Akpabio
A baya, mun ji cewa Gwamna David Umahi ya hakura da takarar kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10, ya koma goyon bayan Godswill Akpabio bisa umurnin Bola Tinubu.
Source:LegitHausang