Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Attahiru Jega sun bude sabuwar jam’iyya.
Sunan sabuwar jam’iyyar da suka bude The National Movement.
Sauran wanda aka bude jam’iyyar dasu sune Farfesa Rufai Alkali, Murtala Nyako wanda tsohon gwamnan Adamawa ne, tsohon na hannun damar shugaba Buhari, Malam Buba Galadima.
Akwai kuma Solomon Dalung, Dr. Usman Bugaje, Farfesa Pat Utomi, Sanata Rufai Hanga, da dai sauransu.
An jima kadanne za’a kaddamar da jam’iyyar a hukumance.