Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Kwankwaso, yace yanzu dukkanin masu takara sun koma talakawa.
Rabiu Musa Kwankwaso yace sauya fasalin takardun kuɗi ya sanya dukkanin ƴan takarar sun koma matsayi guda ta fannin ƙarfin aljihu.
Sai dai Kwankwaso yace sauya fasalin kuɗin ba abu bane mai kyau duba da yadda ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala.
Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam’iyya mai kayan marmari, (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa sauya fasalin takardun kuɗi ya sanya dukkanin ƴan takara sun zama talakawa.
Rabiu Kwankwaso ya ƙara da cewa cikin sauƙi zai kayar da abokan takarar sa tun da yanzu matsayin su guda ta fannin ƙarfin aljihu.
Rahoton Premium Times Yanzu Kowane Ɗan Takara Ya Koma Talaka -Rabiu Kwankwaso
Ɗan takarar ya bayyana hakan ne a birnin Maiduguri na jihar Borno a ranar Laraba, inda yace mutane da dama na tsokanar sa ya fito takara baya da kuɗi.
“Na sha jin mutane na tsokana ta cewa Rabi’u Ƙwankwaso baya da kuɗin yin yaƙin neman zaɓe, yau sai ga shi shugaban ƙasa ya sanya mu duka masu takarar mun zama talakawa.
Don haka yanzu mu talakawa ne sannna matsayin mu ɗaya.”
A cewar Kwankwaso
Da yake magana kan yiwuwar samun nasarar sa a zaɓen dake tafe, Kwankwaso yace ya nuna ƙwarewar sa lokacin da yayi gwamnan sau biyu a Kano, minista da sanata.
Ya bayyana cewa ƴan Najeriya ba za su zaɓi jam’iyyun APC da PDP ba saboda ba su da wani sabon abun da za su ba ƴan Najeriya.
Sai dai, Kwankwaso, yace sauya fasalin takardun kuɗin ba abu bane mai kyau ga ƙasar nan.
“Abinda kawai na sani shine sauya fasalin kuɗi ba abu bane mai kyau ga ƙasar nan.
Ƴan Najeriya sun cancanci su yi rayuwa cikin zaman lafiya da ƙauna daga shugabannin su.
Amma jefa ƴan Najeriya cikin wahala, ba abu bane mai kyau har ta ga su kan su shugabannin.”
A wani labarin na daban kuma, mun kawo muku jerin sunayen wasu ƴan takara bakwai da suka mutu ana dab a fara zaɓen wannan shekarar.
Ƴan takarar dai sun fito a jam’iyyu daban-daban na ƙasar nan.
Source:LegitHausa