Hukumar zaben kasar Libya tace mutane 61 suka gabatar da takardun su na neman tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za’a gudanar a ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa.
Hukumar tace daga cikin wadanda suka gabatar da takardun su kafin rufe karbar takara a yammacin litinin, akwai Firaminista Abdelhamid Dbeiba da shugaban majalisar dokoki Aguila Salah da Fathi Bashagha, tsohon minista a gwamnatin rikon kwaryar kasar.
Sauran fitattun ‘Yan takara sun hada da Janar Khalifa Haftar da ya dade yana yaki domin kwace ragamar jagorancin Libya da kuma Seif al-Islam Ghadafi, wanda ‘da ne ga tsohon shugaban kasa Muammar Ghadi.
Masu gabatar da kara na soji sun bukaci hukumar zaben da ta dakatar da tantance Janar Haftar da Seif al Islam har sai sun amsa tuhumar da ake musu.
Janar Haftar na fuskantar tuhumar laifuffukan yaki a kasar Amurka, yayin da kotun hukunta manyan laifuffuka ke neman Ghadafi tun daga shekarar 2011 saboda cin zarafin Bil Adama da kuma laifuffukan yaki.
Ana saran gudanar da zaben shugaban kasar ne a ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa.
Tun bayan kashe shugaba Muammar Ghadafi a shekarar 2011, kasar Libya ta fada cikin tashin hankalin da yayi sanadiyar rasa dubban rayuka, yayin da kasar ta zama dandalin Yan bindiga da masu aikata laifuffuka, ciki harda cinikin mutane.