‘Yan sanda sun samu nasarar ceton dukkanin mutanen da ‘yan bindiga suka sace daga rukunin gidajen ma’aikatan Jami’ar birnin Abuja a ranar Talata.
Kafin ‘yan sanda su kubutar da su dai sai da ‘yan bindigar suka nemi a biya su kudin fansar da ya kai naira miliyan 300, kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa dasu.
Sai dai da safiyar yau Juma’a, wani jami’in jami’ar ta UNIABUJA ya sanar da ceto ma’aikatan nasu da ‘yan sanda sukayi ba kuma tare da biyan kudin fansa ba.
Zalika rundunar ‘yan sandan dake kula da shiyyar ta hannun mai Magana da yawunta DSP Josephine Adeh, ta tabbatar da sakin mutanen ba tare da yin karin bayani ba, illa kama wasu dake da hannu a cikin ta’asar da tace an yi.
A wani labarin na dabanr rundunar Sojin Najeriya ta tủra wata tawagar zaratan sojin ta mata guda 100 domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro akan hanyar Abuja zuwa Kaduna wanda ya yi kaurin suna sakamakon hare haren da barayi da kuma masu garkuwa da mutane ke yi.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai ya yaba da matakin wanda yace zai taimada wajen samar da tsaro akan hanyar.
El Rufai ya sha alwashin cewar girke dakarun zai taimakawa matafiya da masu zama a yankunan, tare da karfafa ‘yam mata wajen shiga aikin soji.
Kwamandan runduna ta 1 ta sojin Najeriya, Manjo Janar Usman Mohammed ya yabawa gwamnatin jihar Kaduna kan irin taimakon da take basu domin gudanar da ayyukan su.