Hukumar kula da gidan yarin Najeriya tace yanzu haka jami’an ta tare da na wasu hukumomin tsaro sun yi kawanya ga wasu yan bindigar da suka kai hari gidan yarin Jos.
Sanarwar da Kwantrola Janar na hukumar dake Najeriya ya bayar ta hannun kakakin sa Francis Enobore yace Yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 5.20 na yammacin yau, inda suka dinga harbi da bindiga har suka shiga ciki.
Enobore yace jami’an su sun nemi taimakon wasu hukumomin tsaro inda suka yiwa gidan yarin kawanya, kuma ana kyautata zaton Yan bindigar na ciki.Jami’in yace nan gaba zasu yiwa jama’a bayanin halin da ake ciki.
A wani labarin na daban daga jos jihar filaton kuma, Allah ya yi wa shahararren mawakin kasar Hausa Alhaji Muhammadu Adamu Danmaraya Jos rasuwa a wannan asabar sakamakon fama da rashin lafiya na tsawon makonni kamar dai yadda wasu makusantansa suka tabbatar.
Marigayi Danmaraya dai ya yi wakoki da dama da suka shafi wayar da kai, sannan kuma suka samu karbuwa matuka a tsakanin al’umma ba wai a Najeriya kawai hatta ma a sauran kasashen da ake amfani da harshen Hausa. Ya rasu yana da shekar 69 a duniya.