A karon farko tun daga shekarar 2017 jam’iyyun ‘yan adawa sun shiga zaben jihohi da na kananan hukumomi a Venezuela, zaben da ya samu halartar tawagar sa ido daga Tarayyar Turai.
Hukumar zaben kasar tace an bude rumfunan zabe tun da karfe 6 na safe agogon kasar kuma za a rufe da karfe 6 na yamma inda ake sa ran sakamako da misalin karfe 2 ko 3 na safe.
Amma sai dai farin jinin jam’iyya mai ci ake ganin abune mai wuya jam’iyyun adawa su iya takuba wani abu a wannan zabe.
‘yan adawa na kasar venezuela dai suna samun goyon bayan amurka da ‘yan kanzagin ta yayin da jam’iyya mai ci ke samun goyon bayan Iran da kawayen ta.
A wani labarin na daban ayyana shugaban Venezuela, Nicolas Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar.
Yanzu haka dai an ayyana shugaba Nicolas Maduro a matsayin wanda zai ci gaba da jagorancin kasar har zuwa nan da shekarar 2025.
Tun dai gabanin fitar da sakamakon zaben, babban mai adawa da Maduro, Henri Falcon ya shaida wa manema labarai cewa, ba su amince da tsaren-tsaren gudanar da zaben ba.
Mr. Falcon ya ce, babu wani zabe da aka gudanar a wurinsu, don haka ya zama tilas a shirya sabon zabe.
Tuni shugaba Maduro ya jinjina wa nasarar da ya samu ta sake shafe wa’adin shekaru 6 akan karagar mulki da ya bayyana a matsayin wani abu mai cike da tarihi.
Sakamakon zaben,ya nuna cewa, Maduro ya samu kashi 67. 7 cikin 100, yayin da Falcon ya samu kashi 21.2.
Sai dai wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar gabanin zaben na jiya, ta nuna cewa, ‘yan takarar biyu na kafa-da-kafa da juna wajen samun yawan kuri’u.