Jim kadan bayan maganar Nyesom Wike, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya yi masa raddi a shafin Twitter.
Gwamna Nyesom Wike ya zargi tsohon shugaban majalisar wakilan da kin cika alkawarin da ya dauka.
Dogara yace Gwamnan na fama da larurar mantuwa, har yana neman tona asirin da babu wanda ya sani.
Rt. Hon. Yakubu Dogara wanda ya sauka daga kan kujerar shugaban majalisar wakilan kasa a 2019 ya maidawa Nyesom Wike martani.
A wasu maganganu da ya yi a shafinsa na Twitter, Hon. Yakubu Dogara ya yi raddi ga Gwamna Nyesom Wike wanda ya zarge shi da yin karamar magana.
Gwamnan na jihar Ribas ya soki Yakubu Dogara bisa zargin cewa ya gagara cika alkawarin da ya dauka, saboda yana goyon bayan Atiku Abubakar.
A zafafan martanin da ya yi, tsohon shugaban majalisar tarayyar yace Gwamnan yana fama da cutar mantuwa da kokarin kakabawa kowa ra’ayinsa.
Dogara yake cewa bai da niyyar yi wa Wike raddi a gidan talabijin, amma idan har shi Gwamnan ya bada dama, zai fallasa sirrin zaman da suka yi tare.
Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto a yammacin ranar Litinin dinnan.
Jawabin Yakubu Dogara a Twitter “Ga ‘dan uwana Nyesom Wike, idan har kana fama da wata larura, ban yi tunanin cutar mantuwa na cikinsu ba.
Meyasa za kayi tunanin cewa babu wanda ya isa ya kama wata matsaya ya rike gam, ba tare da ya sauka daga kanta ba? Abin takaici ne a ce ka gagara tuna dalilin zamanmu.
Meyasa ra’ayin ka ne kadai za a girmama, shi kadai ne abin bi?
Ba zan taba cin amanar wani ‘danuwa ba, shiyasa ba zan je gidan talabijin domin in maida maka martani ba.
Sirrin tattaunawarmu yana tsakani na da kai, amma idan kana ganin za a iya fallasawa Duniya, ka bani dama a rubuce Daga nan zai shaidawa jama’a abin da ya wakana domin su zama alkalai, suyi mana shari’a a kan wa yake fadan gaskiya.
Na godewa Ubangiji da ya sa akwai wanda zai iya bada shaida.” – Hon. Yakubu Dogara
Takarar Idahosa a NNPP Kun samu labari Bishof Isaac Idahosa yace ya na zaune a Legas wata rana, sai Rabiu Musa Kwankwaso ya kira shi a wayar salula cewa yana nemansa.
Faston ya shaidawa manema labarai daga zuwa Abuja bayan nan, sai aka bijiro masa da maganar zama ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa a 202