Barista Abba Hikima, lauyan Gamaiyar Masu Tuƙa Baburan Adaidaita-sahu na Jihar Kano, ya koka cewa gwamnatin jihar ba ta da niyyar sasantawa da matuƙa baburan.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ranar Litinin ne dai ƴan adaidaita-sahun su ka tsunduma yajin aiki domin nuna rashin goyon bayan yadda hukumar KAROTA ta ce sai sun biya kudi Naira 8,500 domin sabunta lambar rijista.
Sun kuma koka kan yadda KAROTA ke karɓar kuɗaɗen haraji barkatai a hannun su, musamman ma naira 100 da su ke biya kullum, inda har ranar Lahadi ma sai sun biya, duk da cewa ma’aikatan karɓar harajin ba sa fitowa a ranar.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na facebook a jiya Talata da daddare, Hikima ya baiyana cewa an kafa kwamitin sulhu, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Kano, Hamisu Chidari.
Batista Hikima ya ce shi ma yana cikin kwamitin sasantawar, amma har a jiya Talata, ba a daidaita da gwamnatin ba sakamakon kafewa da ta yi a kan matsayar ta.
“A matsayina na lauyan gamayyar masu tuka bubaran Adaidaita sahu na jahar Kano, kuma daya daga cikin wakilan su a sulhun da ake sa ran yi da gwamnatin jahar Kano, ta hanyar Kakakin Majalisar Dokokin Jahar Kano, ina mai sanar da jama’a cewa har yanzu daren Talata 11/1/2022, ba a samu wata matsaya da gwamnati ba sakamakon kafewa da gwamnatin tayi na akan matsayar ta.
“Sabo da haka duk kokarin da wasu suke yi na yada farfaganda cewa an janye wannan yajin aiki to suna magana ne ba da yawun wadanda suka kira wannan yajin aiki ba,” in ji Hikima.
Hikima ya kuma yabawa matuƙa Baburan Adaidaita-sahu a bisa jajircewar da su ka yi wajen tafiya yajin aikin bisa bin doka da oda.
“A karshe ina so inyi amfani da wannan dama in jinjinawa matuka wadannan babura domin juriya da suke nunawa cikin bin doka da sanin ya kamata,” in ji shi.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa yayin da yakin aikin ya shiga rana ta uku, tuni dai al’umma a birnin Kano ke ji a jikin su, musamman marasa ababen hawa.
Haka kuma jaridar nan ta gano cewa harkar sufuri ta Achaba ta dawo a fakaice, in da kuma masu ƴar ƙurƙura su ka maida ita ta haya a cikin birnin da kewayen sa.