Kafafen yada labaran duniya sun bayyana yadda suka fahimta dangane da atisayen tauna tsakuwa domin aya taji tsoro da sojojin sama, ruwa, dama kasa suka gudanar a satin daya gabata.
Reuters ta rawaito cewa Iran din ta gargadi amurka data janye sojojin ta daga kusa da inda take gudanar da atisayen ta a tekun fasha (Persian Gulf).
An kammala atisayen ne a ranar talata, satuttuka kafin dawowa tattaunawar janye takunkuman tattalin arziki tsakanin Iran da saukan manyan kasashen duniya.
Hial ta sanar da cewa Iran ta gargadi amurka da zuwa kusa da inda take aiwatar da atisayen.
Mai magana da yaun CENTOCM yace ”Muna sane da yadda ake boye bayanai daga majiyoyin Iran”.
Kafar yada labarai mallakin jamus, SPIEGEL ta bayana cewa; Iran ta bayyana cewa bata dauke da wata barazana ga kowacce kasa a yankin , sai dai tana atisayen ne saboda shirin ko ta kwana”.
Amma sai dai kasashen yankin tekun fasha musamman na labarabawa suna ganin atisayen na Iran a matsayin barazana musamman a yankin da kaso arba’in na danyen man fetur din duniya yana fita daga nan ne, a kwai kuma tunanin cewa Iran din tana iya kaima haramtacciyar kasar Isra’ila hari da makaman ta masu cin matsakaicin zango har na kilomita 2200.
Bloomberg ta sanya dangon ta cewa; Iran ta kakkabo makaman amurka yayin atisayen ta kuma ta gargadin amurka bisa keta sararin samaniyar ta da makman ta sukayi.
Jaridar Newsweek; Iran ta harba makamai masu linzami a wani salo na wasan yaki kan makaman amuka yayin atisayen ta.
Jaridar Al’arabiya; Iran ta soma atisaye sati daya kafin fara tattaunawar makamashin nukiliya.
Alsharq Alauwat; Iran tayi gagarumin atisaye a kudancin iyakar ta.
Middle East; Yadda Iran take atisaye a tekun Oman yayin da ake tsaka da samun sabani tsakanin ta da amurka.
Sky News Arabin; Sabon sabon nuna isa, Iran ta fara atisayen sararin smaniya na kwana biyu.
Arabic21; Manayan atisaye wanda ya shafe rabin Iran na kwana biyu.
Aljazeera; Shirin makamashin nukiliyar Iran, Iran ta bayyana sharuddan ta domin komawa teburin tattaunawa a dai dai lokacin da sojojin ta keyin atisaye.
Israel News24 ta rubuta cewa;Iran ta harba makamin ”Zulfiqar1440” a atisayen gabashin mashigar ruwan hormuz.
Sa’annan kafar yada labarai ta This newa ma ta wallafa cewa; Iran ta gargadi amurka dangane da atisayen ta a tekun fasha.
Jaridar kasar kuwait, Aljarida ma ta bayyana cewa Yadda atisayen Iran yake wakana da kuma gargadin yaki mai tsada ga Isra’ela.
RussianAlium ma ta bayyana cewa Iran ta gabatar da atisaye da tsarin sojin ta.
Almanar Iran; iata kuma ta bayyana 15 khurdad da kuma mirsad sun tabbatar da samun cikakken tsaro ga Iran.
26epwebsite daga yemen kuma suna wallafa cewa; Atisayen zulfiqara yab cigaba a rana ta biyu.
SpunikaArabic sun wallafa cewa; Iran ta gudanar da atisayen ta tare da hadin gwuiwar gabadayan sansanonin sojin saman kasar.
Almayadin ta wallafa yadda sojin Iran suka kakkabo makamai masu linzami na amurka yayin da suka shiga sansanin atisayen.
Jaridar Alnahar ta egypt kuma ta bayyana cewa Iran ta fara atisayen kwana biyu.
Alkhaleej Online ta bayyana wannan atisaye a matsayin na zaman lafiya da abota inda ta bayyana cewa Iran ta fara atisayen kwana biyu.
Jaridar larabci mallakin turkiyya, yeni safak ma ta bayyana cewa, Iran ta bayyana kakkabo makaman amurka guda biyu yayin atisaye.
Kafar yada labarai dafalasdinu, Sama ta bayyana cewa Iran ta aiwatar da manyan atisaye a ”Red sea” kuma ta bayyana cewa duka wani kuskure daga kowacce kasa zai gamu da amsa mai kaushi.
Kafar yada labaran sojin haramtacciyar kasar isra’ela sun, Debkafile sun bayyana wasu kayan aiki da akayi amfani dasu wajen yin atisayen kuma sun bayyana cewa atisayen yayi karo da abinda ta kira da kama wasu mutum biyar masu shirin aiwatar da ta’addanci a afirkan.
Kafar yada labaran Isra’ela ta Ma’ariu ta rawaito labarin dangane da gargadin Iran ga amurka.