Labarai marasa dadi sun ishe majiyar mu kan yadda a jiya talata jami’an tsaron ‘yan sanda sukayi dirar mikiya kan bayin Allah, fararen hula ‘yan najeriya kuma wadanda basu dauke da makami kurum domin sun fito suna gudanar da ibadar su kamar yadda sukayi imani.
Lamari ne wanda ya shafi ‘yan uwa almajiran malam zakzaky, wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a kuma mambobin harkar musulunci a najeriya.
Labarin yadda lamarin ya faru na sanya tashin hankali gami da firgici a zuciyar wanda ke neman kwatanta adalchi tsakanin ‘yan najeriya mabiya mabambantan addinai, akidu da fahimtoci.
Kusan a duk fadin garuruwan najeriya an gudanar da wani taro da ‘yan shi’an suke kira da ”Tattaki” wanda suka bayyana cewa sukan aiwatar da wannan taro na tattaki ne domin tunawa da waqi’ar ashura da ta faru a tarihin musulunci a shekara ta 61 bayan hijirar manzon rahama (S.a).
Littafan tarihin musulunci sun fayyace dalla dalla yadda aka kashe jikan manzon Allah (S) a dajin karbala, ga mai bukatar sanin yadda lamarin ya faru yana iya komawa ya karanta littafan tarihin musulunci na sunnaj da shi’a, musamman ma shahararren littafin nan wanda ya kawo kusan komi dangane da wannan waqi’a ta zariy mai suna ”maqtal” wanda aka rubuta da harshen larabci.
Hatta da harsunan hausa da turanci ma anyi rubuce rubuce masu dimbin yawa dangane da wannan waqi’a ta ashura.
A bayanin mabiya malam zakzaky sun tabbatar da cewa sukan fito ”Tattaki” ne domin tunawa da wannan rana amma abin yana basu mamaki yadda jami’an tsaro a lokuta dama sukan dira musu da harbe harbe da harsasai masu rai kuma hakan kan zama sanadiyar rasa rayukan da dama daga cikin su.
Abinda yafi bama ‘yan shi’ar mamaki kuma ya daure musu kai shine, shin gwamnatin najeriya da ba ruwanta da addini ko akidar mutum ce bata son wannan taro na ”Tattaki” ko kuma a kwai sa hannun wata kasar ta ketare?
Ko kuma dai saudiyya?