An yi zama da mutanen Gwamna Nyesom Wike domin shawo karshen matsalolin dake damun PDP.
Rahoto ya nuna ‘Yan bangaren Wike suna so a sauke Iyorchia Ayu daga kujerar shugaban PDP na kasa Gwamnoni masu-ci da tsofaffin Gwamnoni sun halarci wannan taron neman sulhu da aka yi a Abuja.
A ranar Lahadin nan da ta wuce, 31 ga watan Yuli 2022, Gwamnan Ribas watau Nyesom Wike ya yi zama da mutanensa da jagororin jam’iyyar PDP.
Daily Trust ta kawo rahoto cewa Mai girma Nyesom Wike ya hadu da masu ruwa da tsaki a PDP da wadanda suka yi masa yakin neman tikiti na zaben 2023.
An yi wannan zama ne a gidan gwamnan Ribas da ke unguwar Asokoro a birnin tarayya Abuja.
Wata majiya daga jam’iyyar ta PDP ta shaidawa jaridar cewa an yi zaman ne da nufin a dinke barakar da aka samu tun bayan zaben fitar da gwani da aka yi.
An samu sabani tsakanin bangaren Gwamna Wike da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda ya sake samun tikitin takara a zaben badi.
Sai an yi waje da Ayu tukuna:
A wajen wannan taro da aka yi a Abuja, mutanen Wike sun bukaci a tsige shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, idan har ana so su goyi bayan Atiku Abubakar.
An ware ‘Yan Kudu a PDP Wani wanda ya halarci taron yake cewa a karkashin shugabancin Dr. Ayu, an maida wani bangare saniyar ware a tafiyar PDP, wanda haka zai kawo cikas a zabe.
‘Yan bangaren Wike da ake kokarin ayi sulhu da su, sun nuna babu ta yadda jam’iyyar PDP za ta iya shiga kudancin Najeriya yin kamfe a yadda ake tafiya.
AIT tace wadanda suka halarci zaman sun kunshi Gwamnonin Oyo, Abia, Benuwai da Enugu, Seyi Makinde, Okezie Ikpeazu, Samuel Ortom, Ifeanyi Ugwuanyi.
Sai Donald Duke, Gabriel Suswam, Olusegun Mimiko, Seriake Dickson, Ibrahim Idris da Jonah Jang.
Babu rabuwar kai:
Gana Farfesa Jerry Gana wanda yana cikin wadanda suka jagoranci yakin neman takarar Wike a jam’iyyar PDP ya shaida cewa wannan ne zaman farko da suka yi.
Tun bayan zaben fitar da gwani, Farfesa Jerry Gana yace ba a iya irin wannan zama ba. An ji Gana yace kansu na hade, kuma za su bayanin halin da ake ciki.
Source:hausalegitng