Majalisar Dinkin Duniya tace, kusan kashi 40 cikin 100 na wasu al’ummar yankin Tigray da ke fama da yaki a kasar Habasha na fama da “matsanancin karancin abinci.
Wasu rahotannin na cewa lamarin ya tilastawa wasu daga cikin ma’aikatan jinya da kuma likitoci a babban asibiti a yankin Tigrai yin bara domin neman abinci.
Daya daga cikin likitocin ya ce, tsawon watanni takwas ba a biya su albashi ba, lamarin da ya jefa su bin wasu hanyoyin da za su tallafa wa iyalansu.
Rahoton wanda shi ne na farko kan tabbataccen kididdigar samar da abinci cikin watanni shida da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya bayyana irin bala’in jin kai a arewacin kasar Habasha, inda dakarun da ke goyon bayan gwamnati da ‘yan tawayen kabilar Tigrai (TPLF) ke fafatawa da juna tun daga cikin watan Nuwambar shekarar 2020.
A wani labarin na daban Hukumar samar da abinci ta duniya ta dakatar da rabon kayan agaji a garin Kombolcha da ke arewacin kasar Habasha, bayan da aka wawure kayayyakin da ta adana, al’amarin da ake zargin ‘yan tawayen Tigray da wasu mutanen yankin da aikatawa.
Ya ce a lardunan Tigray, Amhara da Afar, kimanin mutane miliyan 9.4 a yanzu suna cikin tsananin bukatar agajin abinci.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum miliyan 5.2 daga cikinsu suna yankin Tigray, inda 534,000 ke a lardin Afar sai kuma miliyan 3.7 da kelardin Amhara.
A cewar MDD barazanar da ma’aikatanta suka fuskanta a yankin, ya sa aka yanke shawarar dakatar da rabon kayan abinci a Dessie da Kombolcha, garuruwa biyu masu muhimmanci kan hanyar zuwa babban birnin kasar, Addis Ababa, tana mai jaddada cewa irin wannan cin zarafi na jami’an jin kai da sojoji ke yi ba abu ne da za a amince da shi ba.
A baya-bayan nan ne dai gwamnatin Habasha ta sanar da cewa ta kwato garuruwan biyu, sai dai sojojin na Tigray sun ce sojojin sun kwato yankunan bayan da ‘yan tawayen suka fice.
Yakin dai ya barke ne a watan Nuwamban shekarar 2020 lokacin da Firayim Minista Abiy Ahmed ya aika da sojoji zuwa yankin Tigray domin su hambarar da kungiyar ‘yan tawayen kabilar Tigrai matakin da ya ce ya zo ne a matsayin martani ga hare-haren ‘yan tawaye a sansanonin sojoji.