Hukumomi a Uganda sun gurfanar da mutane 15, ciki har da wata mace mai juna biyu gaban kotu bisa zargin su da bada gudunmawa ga ‘yan tawayen kasar da suka tayar da wasu tagwayen bama-bamai a babban birnin kasar.
A baya-bayan nan dai, Uganda ta sha fama da hare-haren tashin bama-bamai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 da kuma jikkata wasu da dama.
Tun a lokacin da lamarin ya faru ne kuma mahukuntan kasar suka dora alhakin faruwar lamarin kan kungiyar ta’addanci mai alaka da ta IS wato ADF.
Haka kuma an tura tarin jami’an tsaro don yi wa sansanin ‘yan ta’addan luguden wuta.
Tun watan Afrilun 2009 ne kungiyar ta ADF ta fara kaddamar da munanan hare-hare a kasar sai dai wannan shine karon farko da aka fara samun tashin bam.
A wani labarin na daban Mahukuntan Madagascar sun sanar da karuwar alkaluman mutanen da suka mutu a hadarin kwale-kwalen farkon makon nan zuwa 85 bayan gano karin gawarwaki 21 yau alhamis a ci gaba da laluben mutanen da suka bace a hadarin.
A cewar shugaban rundunar ‘yan sandan Madagascar da ke tabbatar da alkaluman ga manema labarai ya ce zuwa yanzu gawarwakin mutane 85 aka kai ga tsamowa.
Wasu bayanai na cewa jirgin kwale-kwalen wanda na dakon kaya ne bashi da izinin jigilar fasinja daga hukumomin kasar.
Mahukuntan Madagascar sun ce kwale-kwalen ya dauki mutanen da suka wuce kima wanda ya kai shi ga nutsewa yana tsaka da tafiya bisa ruwa.
Baya ga hadarin jirgin kwale-kwalen dai kwana guda tsakani Madagascar ta sake gamuwa da hadarin jirgin Shalkwafta wanda ke dauke da manyan jami’an gwamnati ciki har da ministan jinkai, wadanda suma suka fada ruwa ko da ya ke ministan ya tsira da ransa bayan ninkayar sa’o’i fiye da biyu a cikin ruwa.