Shugaban kasar Tunisiya Kais Saied ya rusa wata Majalisar koli mai zaman kanta da ke sa ido kan shari’a a kasar, yana zarginta da nuna son kai, a wani mataki na baya bayan nan da ya janyo cece-kuce tun bayan korar gwamnatin kasar a bara.
Tun a ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata, Saied ya kara karfin ikonsa, lokacin da ya kori gwamnati tare da narke majalisar dokokin kasar.
‘Yan Tunisiya da dama sun yi maraba da matakin da ya dauka na adawa da tsarin siyasar da aka kwatanta da na cin hanci da rashawa da kuma rashin karsashi.
Amma jiga-jigan ‘yan siyasa da kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi gargadin na iya zama mulkin kama karya, matakin da shugabannin duniya suka nuna matukar damuwa.
A wani mataki da ake sa ran zai kara haifar da tashin hankali, Saied da sanyin safiyar Lahadi ya sanar da rusa majalisar koli ta shari’a (CSM) yayin wata ganawa da ministocin gwamnati.
A wani labarin na daban Dubban ‘yan Tunisia ne suka taru a kusa da majalisar dokokin kasar a yau Lahadi domin nuna adawa da kwace ikon mulkin shugaban kasa da suka kira juyin mulki.
Wannan dai shi ne gangami na baya-bayan nan da ke adawa da matakin da shugaba Kais Saied ya dauka a ranar 25 ga watan Yuli na korar gwamnati, dakatar da majalisar dokoki da kuma kwace madafun iko, saboda wata babbar barazana ga kasar da aka fara boren kasashen Larabawa na nuna adawa da mulkin kama karya a shekara ta 2011.
Masu zanga-zangar sama da 3,000 ne suka taru, suna ta kururuwar cewa su na son a kawo karshen juyin mulkin da kuma aikin shugaba Kais da ke kokarin haifar da yakin basasa, tare da bayyana shugaban kasar a matsayin “wakilin mulkin mallaka.
Kamfanin dillancin labarai na Faransa, ya ruwaito cewa wasu daga cikin fusatattun masu zanga-zangar na dauke da alluna da ke nuna adawa da yiwa kafafen yada labarai barazana da kuma neman Hukumar shari’a mai zaman kanta.