A ranar lahadi 12 ga disambar wannan shekarar ne aka gabatar da tarukan tunawa da kisan kiyashin zariya a fadin duniya.
Kisan kiyashin zariya wani lamari ne wanda ya faru a birnin zariya dake arewacin najeriya mahaifar jagoran harka islamiyya, sheikh ibrahim zakzaky.
Zaiyi wuya sosai ace an iya mancewa abinda ya faru a zariya shekaru shidda da suka gabata.
An shafe iyali, an kashe maza, mata, kananan yara harma da tsofaffi.
Kusan ana kiyasin an kashe daruruwam mutane a wannan hadisa ta zariya, tun bayan kisan kiyashin zariyan ake tsare da jagoran ‘yan uwa musulmi sheikh ibrahim zakzaky kafin ya samu ‘yancin sa bayan da kotu ta sake shi a watannin baya.
Kamar yadda ‘yan uwa musulmi suka saba wannan karon ma sun gudanar da taron tunawa da wannan hadisa ta kisan kiyashin zariya kuma an gabatar da wannan taro a sassan duniya baki daya ciki har da najeriya, dama babban birnin tarayya na abuja.
Taron tunawa da waqi’ar zariya wanda aka gudanar a abuja ya samu halartarmutane daga sassa daban daban na najeriya inda bayan wakokin tunawa da waqiar aka saurari muhadarori daga wasu daga cikin manyan malamai daga sassa daban daban na najeriyar.
A nasa bangaren jagoran harkar musulunci a najeriya sheikh ibrahim zakazky ya gabatar da bayanin sa ta hanyar yanar gizo gizo inda yayi gajeren bayani mai gamsarwa gami jan hankalin al’ummar najeriya dama duniya gabaki daya kan taimakon raunana da kuma hana zalunci.
Inda daga karshe shehin malamin ya godewa mahalarta taron kuma ya basu dakon da zasu isarwa al’umma na cewa lallai addinin Allah zai dawo yayi iko da wannan kasa tamu ta najeriya.
Ranar 12 ga disambar kowacce shekara dai ya zama wata rana wacce ba za’a mance da ita ba a fagen tarihi kuma za’a tuna da wadanda aka zalunta za kuma a tuna da wadanda sukayi zalunci.