Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tsohon Shugaban kasar, Goodluck Ebele Jonathan a fadar Villa.
Jonathan ya je fadar shugaban kasar ne bayar da jawabi a kan rikicin shugabancin da ke faruwa a kasar Mali.
Idan za ku tuna, tawagar ECOWAS da Jonathan ya jagoranta sun sauka Bamako babban birnin Mali a ranar Talata domin shiga tsakani Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tsohon Shugaban kasar, Goodluck Ebele Jonathan a yau Juma’a, 28 ga watan Mayu, a fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya, Abuja.
Jonathan ya ziyarci Shugaban kasar ne domin ba shi bahasi a kan rikicin shugabancin da ke faruwa a kasar Mali kamar yadda hadimin Shugaban kasa a shafukan zumunta na zamani,
Ya kuma bayyana cewa wata tawagar ECOWAS da Jonathan ya jagoranta sun sauka Bamako babban birnin Mali a ranar Talata domin shiga tsakani. Ya wallafa a shafinsa: “Shugaban kasa @Mbuhari ya tarbi tsohon Shugaban kasa @GEJonathan yau.
Jonathan kasar ya kasance a Fadar Shugaban Kasa, Abuja don yi wa Shugaban kasar bayani game da sabon rikicin siyasar kasar ta Mali.
“Wata tawagar ECOWAS karkashin jagorancin GEJ ta kasance a Bamako, babban birnin Mali ranar Talata, don sasantawa.”
Da yake tabbatar da ganawar tasu, Shugaba Buhari ya ce: Na hadu da tsohon Shugaba Jonathan a safiyar yau, game da halin da ake ciki a Mali, inda shi ne wakili na musamman kuma Mai shiga tsakani na ECOWAS.
Ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hallara domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da tsaro a kasar ta Mali.
Ba za mu iya ɗaukar ci gaban wannan rikici ba. Legit.ng ta tattaro wasu martanin da jama’a suka yi kan ziyarar.
Inda da dama suka yi ta bayyana albarkacin bakin su dangane da ziyarar a kafafen sada zumunta na zamani, wasu na yabawa wasu kuma na sukan ziyarar