Tsohon shugaban Kasar Afirka ta kudu, farar fata na karshe da ya jagoranci kasar, Frederik de Clerk ya rasu yau alhamis yana da shekaru 85 a duniya.
A ranar 2 ga watan Fabarairun shekarar 1990, tsohon shugaba Frederick de Clerk ya dage haramcin da aka yiwa Jam’iyyar ANC ta Nelson Mandela da wasu kungiyoyin faftukar karbar ‘yanci a Majalisar dokokin Afrika ta Kudu tare da sakin Mandela da aka tsare na shekaru 27 a gidan yari, matakin da ya baiwa bakaken fata damar shiga siyasar kasar da kuma samun shugaban kasa bakar fata na farko, wato Mandela.
De Clerk ya bayyana cewar yana fama da cutar kansa ko kuma sankara a ranar 18 ga watan Maris na wannan shekara, lokacin da ya cika shekaru 85 a duniya, yayin da Gidauniyar sa ta sanar da cewar cutar sankarar ce tayi sanadiyar mutuwar ayau bayan ya dade yana fama ad ita.
Sanarwar tace tsohon shugaban ya rasu ya bar iyalin sa Elita da ‘yayan sa Jan da kuma Susan, tare da jikoki, kuma nan gaba kadan iyalan zasu sanar da yadda jana’izar sa zata gudana.
An haifi Frederick de Clerk a Johannesburg daga cikin mutanen da ake kira Afrikaners, wato fararen fatar da suka fito daga Netherlands suka kuma yiwa kasar mulkin mallaka, yayin da mahaifin sa ya zama dan majalisar dattawa a gwamnatin masu nuna wariyar jinsi, kuma ya rike mukamin shugaban kasa na wucin gadi na dan gajeren lokaci.
Tsohon shugaban yayi karatun aikin lauya a jami’a, kafin ya lashe kujerar dan majalisa a karkashin jam’iyyar da ta aiwatar da manufofin wariyar jinsi.
De Klerk ya rike mukaman ministoci da dama, kafin ya zama shugaban kasa a shekarar 1989, mukamin da ya rike har zuwa lokacin da ya mika mulki ga zababben shugaba kasa Nelson Mandela a zaben dimokiradiyar kasar na farko a shekarar 1994.