Kungiyar Tinubu/Shettima Network (TSN) 2023 ta na so kowa ya hakura da takara, a sallamawa APC Shugaban TSN 2023, Dr. Kailani Muhammad ya ce Bola Tinubu ya fi kowa dacewa da rike mulkin Najeriya.
Saboda haka ne Kailani Muhammad ya roki ‘Yan takaran PDP, LP da NNPP su janye takarar da suke yi.
A lokacin da ake shirye-shiryen zaben shugaban kasa a Najeriya, sai ga shi wasu masoyan Bola Ahmed Tinubu su na neman a sallama masa.
Daily Trust ta rahoto cewa kungiyar Tinubu/Shettima Network (TSN) 2023 ta nemi sauran ‘yan takaran shugaban kasa su janyewa Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Tinubu/Shettima Network (TSN) 2023 na kasa, Dr. Kailani Muhammad ya yi wannan kira na musamman da yake bayani ne jiya a birnin Abuja.
A ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba 2022, Dr. Kailani Muhammad ya rantsar da shugabannin kungiyar su ta magoya bayan Tinubu na fadin Najeriya.
TSN 2023 ta samu ofis a Abuja Haka zalika rahoton ya ce kungiyar TSN ta bude babban ofishinta da yake birnin tarayya Abuja.
Shugaban wannan kungiya ta mogaya bayan Bola Tinubu/Kashim Shettima yana ganin abin da ya fi dacewa da sauran ‘yan takara shi ne su hakura.
Bola Tinubu wajen kamfe Hoto: guardian.ng Asali: UGC Wahalar banza suke yi…
Kailani Muhammad ya ce zai fi kyau ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na LP da Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP su daina bata lokacinsu.
A ra’ayin shugaban Tinubu/Shettima Network (TSN) 2023 na Najeriya, abokan gwabzawar Tinubu a zaben na badi su na yin asarar dukiyarsu ne.
Da yake bude babban ofishinsu a jiya, Kailani Muhammad ya nuna sauran ‘yan takaran shugaban kasar sun cancanta, amma Tinubu ya fi su dacewa.
Saboda haka ne ya yi kira ga masu harin mulkin Najeriya da su jinginar da wannan buri da suke da shi, su goyi bayan takarar da Tinubu yake yi a APC.
“Mun san cewa sauran masu neman kujerar shugaban kasa su na da kima, amma Asiwaju Ahmed Tinubu ya fi dukkaninsu daraja. Saboda haka su janye takararsu, su mara masa baya a takarar shugabancin kasar da yake yi.” – Dr. Kailani Muhammad.
An ji labari Nyesom Wike da sauran ‘Yan G5 da kuma Bode George, Donald Duke, Jonah Jang, da Olusegun Mimiko sun zauna da Bola Tinubu a Landan.
Jiga-jigan jam’iyyar hamayyar za su goyi bayan Tinubu a kan ‘dan takararsu watau Atiku Abubakar, da sharadin APC za ta sallamawa ‘yan takaran PDP.