Ana samun karin yan majalisar tarayya da a yanzu ke goyon bayan tsige Shugaban Najeriya.
Muhammadu Buhari Daya daga cikin wadanda ya nuna goyon bayansa kan kirar neman tsige shugaban kasar shine Sanata Elisha Abbo na jam’iyyar APC a ranar Juma’a 29 ga watan Yuli.
A ra’ayin Abbo, Shugaba Buhari ya sauka daga mukaminsa saboda ya gaza tsare rayyuka da dukiyoyin yan Najeriya.
Sanata Elisha Abbo, dan majalisar tarayya daga Adamawa North ya goyi bayan kiran da sanatocin jam’iyyun adawa suka yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari.
Abbo ya bayyana matsayinsa ne kan batun tsige shugaban kasar a wurin taron shugabannin kiristoci na Arewa da aka yi a ranar Juma’a 29 ga watan Yuli a birnin tarayya, Abuja.
Sanatan ya fada wa yan jarida cewa dalilinsa na goyon bayan kiran tsige shugaban kasar shine mummunan halin rashin tsaro da ake ciki a kasar.
A cewar dan jaridar, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gaza wurin sauke nauyin da aka dora mata na farko wato kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.
Lamurra dai sun tabarbare sosai a Najeriya musamman lamurrran tsaro gami da tattalin arziki wannan ya sanya ‘yan majalisar ke kokarin tsige shugaban kasan wanda wa’adin ke gaf da karewa.
Labarai daga majalisar kasa dia na nuna da cewa da yawa daga ‘yan majalisan ciki har da ‘yan jam’iyyar da shugaba Buhari ya fito na goyon bayan wannan kuduri.
Dakaci karin bayani …
Source:hausalegitng