Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya dakatar da duk wani nau’in sana’ar cajin waya a kananan hukumomi 19 na jihar, saboda dalilai na tsaro
Ya ce gwamnati ta yanke shawarar daukar matakin hana kasuwan cin ne, sabida lura da cewa masu aikata laifukan suna amfani da sana’ar don samun bayanai, musamman masu ba da labaran sirri ga ‘yan bindigan.
A wani labarin na daban kuma daga kasar sin daga ranar 15 zuwa 27 ga watan Satumba ne, za a gudanar da gasar wasanni ta kasar Sin karo na 14 a lardin Shaanxi dake yankin arewa maso yammacin kasar.
Haka kuma ita ce babbar gasar wasanni a kasar Sin.
Ana gudanar da manyan wasanni 35 da kananan wasanni 409, karkashin wannan gasa. Galibin ‘yan wasan guje-guje da tsalle na kasar Sin da suka taka rawar gani a gasar wasannin Olympics ta birnin Tokyon kasar Japan, za su halarci