Tsohon gwamnan Jihar Lagos Bola Ahmad Tinubu kuma jagoran Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya soke taron bikin cika shekaru 70 da haihuwarsa da aka shirya gudanarwa a birnin Lagos a yau saboda nuna alhini ga mutanen da suka jikkata da wadanda suka rasa rayukansu.
Tinubu da ke cikin masu neman samun tikitin tsayawa takarar zabe mai zuwa ya ce a matsayinsa na daya daga cikin dattawan kasa, bai dace ace yana gudanar da bukukuwa a daidai lokacin da wasu ke juyayin rashin ‘yan uwansu ko kuma samun raunukan da suka yi ba.
Saboda haka tsohon gwamnan ya sanar da soke bukukuwa nan take, inda ya bukaci kowa ya koma gidansa bayan ya yi wa jama’a godiya.
A wani labarin na daban kuma Tsohon Gwamnan Jihar kano dake Najeriya Rabiu Musa Kwankwaso ya kawo karshen zamansa a cikin Jam’iyyar PDP sakamakon sanarwar da yayi na ficewa daga cikin ta.
Tsohon gwamnan ya ce sakamakon wasu dalilai na rashin fahimtar juna, ya yanke hukuncin ficewa daga jam’iyyar daga yau Talata, 29 ga watan Maris na shekarar 2022.
Kafin dai wannan lokaci an dade ana rade radin cewar Kwankwaso zai sauya sheka zuwa Jam’iyyar NNPP domin tsayawa takarar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Tuni wasu daga cikin magoya bayan sa suka fice daga PDP domin komawa sabuwar Jam’iyyar a Jihar Kano da kuma wasu jihohi dake cikin kasar.