Shugaban kasa Bola Tinubu ya sallami ministoci biyar a wani yunkuri na sake fasalin majalisar ministocin da ya sanya aka sake tura wasu 10 aiki.
An kuma ba da sunayen sabbin mutane bakwai don zama ministoci a gwamnatinsa.
Hakan na zuwa ne yayin da ya kuma nada Sunday Akin Dare a matsayin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin sadarwa da wayar da kan jama’a da ke aiki daga ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta kasa.
Duba nan:
- Amurka na neman karin kasuwancin da Najeriya
- Tinubu ya Bayyana shirin Rage amfani da Dala a Tattalin Arzikin
- BREAKING: Tinubu sacks five ministers, reassigns 10
Ministocin da aka kora:
Uju-Ken Ohanenye, ministar harkokin mata.
Lola Ade-John, ministar yawon bude ido.
Prof Tahir Mamman, SAN, Minister of Education.
Abdullahi Muhammad Gwarzo, Karamin Ministan Gidaje da Birane da Ci Gaba.
Dr. Jamila Bio Ibrahim, ministar ci gaban matasa.