Legas – Jagoran All Progressives Congress APC, Bola Tinubu, na cikin koshin lafiya kuma ba rashin lafiya yake ba, mai magana da yawunsa, Tunde Rahman, ya bayyana.
Rahaman ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan jihar Legas ya tafi kasar waje ne doomin ganawa da wasu abokan huldan sa game da takarar kujeran shugaban kasan da yake niyyar yi a 2023.
Tinubu ganawa da wasu yaje yi Landan, ba jinya ba: Hadiminsa ya bayyana ranar da zai dawo Hadimin ya bayyana hakan ne a sakon SMS da ya turawa jaridar Punch ranar Juma’a.
Yace: “Asiwaju bai tafi UK don hutu ko rashin lafiya ba. A can yake ganawa da wasu kan abubuwa masu muhimmanci.”
“A gida ko a waje, Asiwaju na aiki koda yaushe. Yawancin mutane ba zasu iya aikin da yake ba. Hakan na nufin yana da karfi da jini sosai.”
“Asiwaju zia dawo Najeriya makon gobe idan ya kammala abubuwa da yake a kasar waje.”
A wani labarin na daban Hukumar samar da abinci ta duniya ta dakatar da rabon kayan agaji a garin Kombolcha da ke arewacin kasar Habasha, bayan da aka wawure kayayyakin da ta adana, al’amarin da ake zargin ‘yan tawayen Tigray da wasu mutanen yankin da aikatawa.
Ya ce a lardunan Tigray, Amhara da Afar, kimanin mutane miliyan 9.4 a yanzu suna cikin tsananin bukatar agajin abinci.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum miliyan 5.2 daga cikinsu suna yankin Tigray, inda 534,000 ke a lardin Afar sai kuma miliyan 3.7 da kelardin Amhara.
A cewar MDD barazanar da ma’aikatanta suka fuskanta a yankin, ya sa aka yanke shawarar dakatar da rabon kayan abinci a Dessie da Kombolcha, garuruwa biyu masu muhimmanci kan hanyar zuwa babban birnin kasar, Addis Ababa, tana mai jaddada cewa irin wannan cin zarafi na jami’an jin kai da sojoji ke yi ba abu ne da za a amince da shi ba.
A baya-bayan nan ne dai gwamnatin Habasha ta sanar da cewa ta kwato garuruwan biyu, sai dai sojojin na Tigray sun ce sojojin sun kwato yankunan bayan da ‘yan tawayen suka fice.
Yakin dai ya barke ne a watan Nuwamban shekarar 2020 lokacin da Firayim Minista Abiy Ahmed ya aika da sojoji zuwa yankin Tigray domin su hambarar da kungiyar ‘yan tawayen kabilar Tigrai matakin da ya ce ya zo ne a matsayin martani ga hare-haren ‘yan tawaye a sansanonin sojoji.