Tawagar yakin neman zaben Tinubu da Shettima, sun yi zama a Abuja inda suka tattauna kan sunayen dake kwamitin.
Sai dai an gano cewa, Sanata Adamu da wasu daga jiga-jigan jam’iyyar APC basu halarci taron ba duk da ya dace a zauna da su.
Simon Lalong ya jagoranci taron inda ya bayyana cewa suna duba sunayen ne domin kwantarwa da gwamnonin APC hankali da wasu mambobin.
Masu tsarin tawagar kamfen din kujerar shugabancin kasa na Tinubu da Shettima sun yi ganawar sirri a Abuja a ranar Talata da yammaci inda suka sake duba jerin sunayen mambobin kwamitin.
Taron da ya samu shugabancin gwamnan jihar Filato, Gwamna Simon Lalong, wanda shi ne darakta janar na kwamitin, an fara shi ba da wuri ba a ofishin PCC dake Abuja.
Wata majiya ta sanar da The Punch cewa ajandar wadanda suka samu halartar taron ta tsaya kan bukatar su sake duba jerin sunayen domin gujewa caccakar da wasu fusatattun gwamnonin APC da mambobin NWC bayan sunayen farko sun bayyana.
Daraktan yada labarai na PCC, Bayo Onanuga, ya tabbatar da hakan ga jaridar Punch kan cewa Lalong ne ya kira taron domin a sake duba jerin sunayen.
“Amma taron cikin gida ne. An yi shi ne domin sake duba jerin sunayen tawagar kamfen din ta yadda jama’a ba za su cigaba da korafi ba. Wannan shi ne makasudin taron.” – Yace.
Sai dai babu wasu mambobin NWC wadanda suka hada da shugaban jam’iyya ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu da ya halarci taron a ranar Talata.
A yayin da aka tambaya ko mambobin NWC ya dace su halarci taron, wata majiya tace in har ba yarjejeniya aka yi ba, suna da hurumin halartar taron.
Yace: “Su ma ai mambobin PCC ne. Ku tuna Adamu shi ne mataimakin shugaban kwamitin sannan wasu mataimakan shugaban jam’iyyar na kasa su ne kodinetocin da mataimakin shugabannin shiyya. ”
”Amma da yawa daga cikinsu basu halarci taron ba. Sai dai na gane cewa akwai taro muhimmi da za a yi na NWC a gobe Laraba domin zantawa kan sunayen.”
A wani labari na daban, ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ba zai samu damar saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta zaben 2023 ba.
Tinubu, wanda a yanzu haka yana kasar Birtaniya, ba zai samu halartar taron saka hannu kan yarjejeniyar da kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) ya shirya ba,wanda shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ke shugabanta.
Source:legithausang