Rahotanni daga babban birnin tarayyar Abuja na tabbatar da cewa tashar talbijin dinnan mallakar jamhuriyar musulunci ta Iran, mai suna Press T.v mai hedikwata a babban birnin Tehran ta shirya tsaf domin hira ta musamman da jagoran harkar musulunci a najeriya, sheikh Ibrahim Yaqoob Al-zakzaky.
Kamar yadda majiyar da samu labari tashar press t.v ta sanar a wasu daga cikin shirye shiryen ta cewa ranar labara zatayi hira da shehin malamin da misalin a gobe laraba 29 da disambar 2021, da misalin karfe 4;30 agogon najeriya.
Ofishin jagoran na ‘yan uwa musulmi na harkar musulunci ma ya fitar da sanarwa dangane da hirar wacce sheikh zakzaky din zaiyi da tashar yada labarai ta Press T.v din.
Wannan dai shine ganawa ta farko da sheikh zakzaky zaiyi da ‘yan jarida wata biyu bayan fitowar sa daga gidan kurkuku, bayan shafe kusan shekaru shidda yana tsare biyo bayan harin kan mai uwa da wabi da sojojin najeriya suka kai gidan shehin malamin a disambar 2015.
Tun disambar 2015 din ne dai mahukunta a najeriya ke tsare da shehin malamin duk da kotuna da suka ta wanke shi amma gwamnatin najeriya tayi kunnen uwar shegu da hukuncin kotun.
Shehin malamin ya samu shakar iskar ‘yanci ne a karshe lokacin da babbar kotun tarayya a kaduna ta sake shi kuma tayi jan kunnen kada a kuma kama shi wanda hakan ya kawo karshen zaman kurkukun shehin malamin na kusan shekara shidda.
Tun bayan fitowar shehin malamin dai ba’a jiyo shi yayi wata magana ta kai tsaye ko akasin hakan da manema labarai ba, illah dai ya gana da wasu ba’adin na ‘yan uwan sa na jini da kuma almajiran sa.
Wannan shine karo na farko da sheikh zakzaky zai gana da ‘yan jaridu tun bayan fitowar sa daga kurkukun, wanda tashar Press T.v mai yada shirye shiryen ta da harshen turanci zata yada kai tsaye.