Aljazeera:
Ba kamar harin da aka kai a baya ba, Iran ta kai hari kan Isra’ila ba tare da wani sanarwa ba, kuma saboda haka Amurka da kawayenta basu da lokaci wajen dakile makaman masu linzami. Makami mai linzami na Fattah shine katin nasara na Iran a wannan aikin.
Duba nan:
CNN:
Bidiyon da aka samu sun nuna cewa makamai masu linzami na Iran sun afkawa Isra’ila.
The Guardian:
Iran ta harba makamai masu linzami kan Isra’ila sa’o’i bayan da Amurka ta yi gargadin cewa Tehran na shirin kai hari.
Duba nan:
- Boko Haram Ta Sace Manoma 15 A Borno
- Burkina Faso, Niger ban French TV show for being ‘contrary’ to values
NBC:
Gobarar makamai masu linzami da Iran ta harba ya haska sararin samaniyar Isra’ila.
Kamfanin dillancin labaran reuters: Yayin da ake harba makamai masu linzami na kasar Iran, an yi ta kara harba bindigogi ta sama a duk fadin kasar Isra’ila, kuma a lokaci guda an ji karar fashewar wani abu a birnin Kudus.
Jaridar Washington Post:
Ma’aikatar tsaro (Yaki) ta Isra’ila ta tabbatar da harin makami mai linzami kan Isra’ila; An yi karar siren hari ta sama; Mutane sun tafi mafaka kuma harshen wuta ya haskaka sararin Isra’ila.